Advert
Home Sashen Hausa A karon farko Gwamnatocin jihohin dake makwaftaka da Dajin Rugu sun fidda...

A karon farko Gwamnatocin jihohin dake makwaftaka da Dajin Rugu sun fidda matsaya daya akan tsaro- Aminu Masari

Gwamna Aminu Bello Masari ya bayyana cewa, a karo na farko, gwamnatocin jihohin dake makwabtaka da dajin rugu, sun dau alkibla daya wajen tunkarar ta’addancin da ya addabi jihohin na Katsina, Zamfara, Sokoto, Kebbi, Kaduna da Naija.

Alhaji Aminu Bello Masari ya fadi haka yau a fadar Gwamnatin Jihar Katsina a jawabin da ya gabatar bayan da ya kaddamar da kwamitin da zai sa ido kan ganin ana amfani, sau da kafa, da dokokin da Gwamnatin Jiha ta kafa domin kawo karshen ta’addanci a wannan jiha.

Gwamnan ya kara da cewa, a yanzu, babu wani abu da gwamnati ta tasa a gaba irin dawo da zaman lafiya tabbatacce a fadin wannan jiha.

Ya kuma yi kira ga ‘yan wannan kwamiti da suyi amfani da matakin ba sani ba sabo wajen gudanar da wannan aiki, kuma suyi kokarin wayar da kan al’umma kan muhimmancin dake akwai wajen dabbaka wadannan dokoki, domin an kafa su ne domin ceto rayuka da dukiyoyin su.

Ya kuma yi kira ga al’umma dasu daure suci gaba da tona asirin masu kai ma ‘yan ta’adda bayanai (informers) da kuma masu kai masu kayan amfanin yau da kullum.

Ta bangaren shi, Shugaban kwamitin Alhaji Sanusi Buba, wanda kuma shi ne Kwamishinan ‘Yan Sanda na jihar Katsina, ya tabbatar wa Gwamna Masari cewa za suyi duk abinda ya kamata domin ganin an cimma burin kafa wannan dokoki, wanda shi ne dawo da zaman lafiya a cikin wannan jiha.

A satin da ya gabata ne, Gwamna Aminu Bello Masari ya sanya hannu a kan wasu sabbin dokoki da za su taimaka wajen yaki da ta’addanci. Dokokin sun hada da na rufe wasu kasuwanni, takaita zirga zirgar ababen hawa, takaita yawan gidajen da za su saida mai a kananan hukumomin da matsalar tafi kamari.

Wakilan kwamitin sun hada da Mai ba Gwamna Shawara a kan sha’anin Tsaro, Wakilan Masarautar Katsina da ta Daura, wakilin rundunar Sojoji, wakilin Hukumar Samar da tsaro ta farin kaya (NSCDC), wakilin hukumar hana sha da fataucin kwayoyi (NDLEA).

Haka kuma a matakin kananan hukumomi, akwai irin wannan kwamiti a karkashin Baturen ‘Yan Sanda (DPO) na karamar hukumar.

✍️S.A Social media Abdulhadi Ahmad Bawa

📸Hoton Gidan gwamnatin Jihar katsina

 

KATSINA CITY NEWShttps://www.katsinacitynews.com
Danjuma Katsina, Dan Jarida, Manazarci, Marubuci, Mamallakin Jaridun KATSINA CITY NEWS, JARIDAR TASKAR LABARAI, THE LINKS NEWS, a karkashin Kamfanin MATASA MEDIA LINKS NIGERIAN LTD

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

Biliyan Ɗari shida da Miliyan ɗari biyu da Hamsin, Tallafi daga Gwamnatin Tarayya domin ɓunƙasa Karkara da gandun Daji a jihar Katsina…..

Biliyan Ɗari shida da Miliyan ɗari biyu da Hamsin, Tallafi daga Gwamnatin Tarayya domin ɓunƙasa Karkara da gandun Daji a jihar Katsina..... A ranar Alhamis...

DIRECTOR-GENERAL INAUGURATES NYSC MEGA PRINTING PRESS

NYSC Director-General, Major General Shuaibu lbrahim today inaugurated the NYSC Mega Printing Press in Kaduna. He said the project, which was conceived almost a decade...

Shugaba Buhari Ya Miƙa Ta’aziyyarsa Ga Iyayen Hanifa, Yarinyar Da Aka Kashe A Kano.

Daga Zaharaddeen Gandu Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya jinjina wa 'yan sandan Jihar Kano game da gano wanda ake zargi da kashe Hanifa Abubakar mai...

REHABILITATION WORK DONE AT THE EKEHUAN ARMY BARRACKS IN BENIN, EDO STATE!

https://www.facebook.com/101788642037662/posts/259649386251586/