A karo na 4 Abba kyari ya gurfana a gaban Kwamitin bincike…

Karo Na Hudu: DCP Abba Kyari Ya Gurfana Gaban Kwamitin Bincike An Kwashe Sa’a 4 Yana Shan Tambayoyi.

– Tsohon kwamandan rundunar IRT, DCP Abba Kyari ya sha tambayoyi na sa’o’i hudu yayinda ya sake gurfana gaban kwamitin binciken kan alakarsa da shahararren madamfari Ramon Abbas wanda aka fi sani da Hushpuppi

Ramon Abbas (Hushpuppi) wanda ake zargi da damfarar wani hamshakin attajiri, ya furta cewa ya ba DCP Kyari cin hanci don kamo wani da ya nemi ya zarce shi a zambar dala miliyan 1.1.

Hukumar bincike ta FBI, wata hukumar tabbatar da doka a Amurka ta zarge shi da hannu a wata harkallar damfara.

Ba tare da bata lokaci ba IGP na yan sanda ya dakatar da DCP Abba Kyari kuma aka saukeshi da jagorancin rundunar IRT.

Kwamitin binciken Kyari da sifeta janar na yan sanda ya kafa karkashin jagorancin DIG Joseph Egbunike, ta zauna ne a hedkwatan FCID dake unguwar Arewa 10 Garki Abuja.

Majiyoyi sun bayyana cewa tun karfe 2 na ranar litinin din jiya da aka shiga yi wa DCP Abba Kyari tambayoyi sai karfe shida na yamma aka tashi.

Wannan shine karo na hudu da zai gurfana gaban kwamitin kuma yana cigaba da jaddada cewa shi kam babu laifin da yayi.

Mi Zaku Ce Kan Wannan?

Jaridar Sokoto

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here