A kwanakin baya, kungiyar gwamnonin Najeriya NGF karkashin

Gwamna Kayode Fayemi, ta kafa kwamiti na musamman domin duba lamarin cire tallafin man fetur.

Za ku tuna cewa shugaban NNPC, Mele Kolo Kyari, ya bayyana a kowani wata ana kashe N120bn don biyan kudin tallafi.

Punch ta rahoto cewa a yayin zaman gwamnonin da ya gudana ranar Laraba, gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i, wanda shine shugaban kwamitin ya gabatar da rahoton bayan tattaunawa da sukayi.

Yayi bayanin cewa ba zai yiwu a cigaba da biyan kudin tallafin mai ba saboda masu fashin kwabri da manyan yan kasuwa kawai ke amfana.

El-Rufa’i yace, “Ana kashe tsakanin N70bn da N210bn kowani wata don kawai a cigaba da sayar da litan mai a N162, wannan ko uwar kudi bai kai ba kuma kudin dake shigowa gwamnati zai ragu da N50bn a kowani wata.”

“Ta wani dalili zamu cigaba da sayar da mai a N162? ”

Ya kara da cewa jihohi 12 kadai ke shan kashi biyu cikin uku na man feturin Najeriya.

A karshe, kwamitin ta bada shawaran cewa a fara sayar da mai a farashin N408.5 ga Lita amma idan kungiyoyin kwadago suka matsa, a sauko da shi N380.

A riwayar Thisday , gwamnonin sun ce a fara sayar da man akalla N385/l.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here