A Jiya Alhamis 12/11/2020 aka fara zaman Shara’a a Babbar kotun Jihar Katsina ta hudu (4) (KATSINA STATE HIGH COURT OF JUSTICE, COURT 4) dake kan haryar zuwa Daura nan cikin Garin Katsina.
Tsakanin
GWAMNATIN JIHAR KATSINA
DA
HAJ. BILKISU MUHAMMED KAIKAI
Tsohuwar mai baiwa Gwamnan Jihar Katsina shawara akan Ilmin ‘Yaya Mata.
Akan zarginta da salwantar da wasu makudan kudade a lokacin tana Mai baiwa Gwamnan Jihar Katsina Shawara akan Ilmin ‘yaya mata a Gwamnatin data gabata.
Tunda farko Lauya mai kare wadda ake kara T. Anjov Esq. Ya shigar da korafi gaban kotun ta hudu (4), ya shigar da korafin “cewa kotun bata da hurumin sauraren wannan karar, akan Zargin da ake yima wadda yake karewa.
Bayan sauraren ba’asin duka bangarorin guda biyu, mai kara da wanda ake kara, daga Karshe Alkalin kotun Mai Shara’a Bawale ya dage cigaba da zaman Shara’ar zuwa 19/11/2020 don yanke hukunci, ko kotun da yake jagoranta nada hurumin sauraren karar koko bata da hurumin sauraren karar?
Rahoto.
Surajo Yandaki
Edita, Mobile Media Crew
13, November 2020.