Home Sashen Hausa A JARIRI DAN SATI BIYU DA MAHAIFIYARSA DAKE HANNUN YAN BINDIGA A...

A JARIRI DAN SATI BIYU DA MAHAIFIYARSA DAKE HANNUN YAN BINDIGA A KATSINA.

A JARIRI DAN SATI BIYU DA MAHAIFIYARSA DAKE HANNUN YAN BINDIGA A KATSINA.

muazu hassan
@ jaridar taskar labarai
Wannan jariri na sama sunan shi Ahmad yana da kwanaki Goma sha biyar da haihuwa, mahara miyagun daji suka kai Hari garin su, mai suna Babban Duhu dake karamar hukumar safana jahar katsina, suka tafi dashi da mahaifiyarshi mai suna lawisa yar shekaru ashirin da biyu.ita ma ga hotonta tare da wannan labarin.
Mahaifin jariri Ahmad kuma mijin lawisa sunansa Rabiu dauda matashi ne da ya gama sakandare.rashin hali ya Sanya ya kasa wucewa sai fara sana a don ya kula da iyalanshi.Baya garin lokacin da maharan suka kai Hari.yana can wani gari wajen kwadago.
Da maharan suka je garin na babban duhu sun tafi da mata Goma sha biyu.hudu daga cikin su duk suna da goyo.kuma suka tafi dasu daji.
Rabi u Dauda ya fada ma jaridun taskar labarai cewa . Wadanda suka tafi da matarsa da jaririn shi sun masa waya sun ce ya tanadi miliyan dari
Shi kuma ya shaida masu cewa bai taba ganin ko dubu dari biyu ba a hannunsa.ko tashi ko ta wani.
Dauda yace sun kara kiranshi suna neman miliyan talatin, yace sai nace masu a in za a hada abin da kowa ya ke dashi a duk fadin babban duhu baya kaiwa miliyan talatin.
Yanzu haka wannan jaririn da mahaifiyarshi sun kwashe kwanaki Goma sha daya a daji hannun wadannan mahara.suna tare da mata Goma sha biyu.
Wadanda abin ya shafa sun bude gidauniyar neman taimako suna tarawa don samun wani abu mai kauri da su ba maharan su sako masu iyalinsu.kamar yadda aka shaida ma jaridun taskar labarai.
______________________________________________
Jaridar taskar labarai na bisa yanar gizo www.taskarlabarai.com da sauran shafukan sada zumunta. Tana da yan uwa jaridar katsina city news dake a www.katsinacitynews.com da kuma the links news dake a www.thelinksnews.com. duk sako a aiko ga 07043777779

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

Amurka za ta fitar da rahoton da ya shafi Yariman Saudiyya kan kisan Jamal Khashoggi-bbc

Amurka za ta fitar da rahoton da ya shafi Yariman Saudiyya kan kisan Jamal Khashoggi-bbc Ana sa ran gwamnatin Biden za ta fitar da wani...

Majalisar Dokokin jihar katsina ta zartar da wa’adin shekara biyar ga wasu jami’an gudanarwa na jami’ar Umaru musa

MAJALISAR DOKOKI TA JIHAR KATSINA TA ZARTAR DA DOKAR WA'ADIN SHEKARA BIYAR TARE DA KARIN SHEKARA DAYA GA WASU MANYAN JAMI'AN GUDANARWAR JAMI'AR UMARU...

HISTORICAL PHOTO NEWS-by MT safana; AN ACCOUNT OF THE BRITISH OCCUPATION OF KATSINA (1903)

HISTORICAL PHOTO NEWS by MT safana AN ACCOUNT OF THE BRITISH OCCUPATION OF KATSINA (1903) "I took the road to Katsina with an escort of sixty...

MUSAN HAUSA; Sunayen Hausawa da ma’anonin su,

*MU SAN HAUSA* *SUNAYEN HAUSAWA DA MA'ANONINSU* *TANKO*: Yaron da aka haifa bayan an haifi mata biyu ko fiye. *KANDE*: Yarinyar da aka haifa bayan an haifi...

TAKARDAR HUKUNCIN KOTU WANDA YA RUSA ZABEN DA AKAYI NA SHGABANCIN JAM IYYAR PDP.

TAKARDAR HUKUNCIN KOTU WANDA YA RUSA ZABEN DA AKAYI NA SHGABANCIN JAM IYYAR PDP. @ Katsina city news Kara ce wadda Abdul aziz lumi ya shigar...
%d bloggers like this: