Dattijo a Jihar Katsina Kuma Raya Karkaran Katsina Alhaji Abu Danmalam Karofi, ya bukaci Gwamnatin Tarayya akan bukatar a tabbatar da kammala aikin daga darajar hanyar Katsina zuwa Kano.

Raya Karkaran na Katsina ya yi wannan Kiran ne a sa’ilinda yake zantawa da manema labarai a Ofishin sa da ke Katsina.

Alhaji Abu Danmalam Karofi ya yi magana Mai tsawo akan muhimmancin wannan hanya ga al’ummomin Jihohin Kano da Katsina ta fuskar inganta tattalin arzikin su.

Ya bayyana cewa Jihohin Katsina da Kano sune suka fi baiwa Shugaban Kasa Buhari kuri’un su a zabukan 2015 da Kuma 2019, a sabili da haka akwai bukatar a kammala aikin domin su san cewa an kula.

Daga nan sai ya roki Gwamna Aminu Bello Masari da takwaransa na Kano Dr.Abdullahi Umar Ganduje, akan su baza kaimi ga Gwamnatin Tarayya, domin ganin an kammala Aikin.

”Labarin da ke zo mana shine kamfanin da ke gudanar da aikin kusan ya kwashe illahirin kayan aikin sa” cewar Raya Karkara.

” A sabili da haka muke roko ga dukkan wadanda aikin ya shafa su bada tasu gudummuwar domin ganin an gudu tare an tsira tare” Inji ADK.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here