A bamu Miliyan Ɗari ko a dauki Gawarwakin su Gobe Talata – Inji Baleri

Daga VOA HAUSA

Shugaban gungun barayin da su ka sace daliban jami’ar Greenfield a Kaduna Sani Idris Jalingo da a ka fi sani da “BALERI” ya yi barazanar hallaka sauran daliban matukar ba a turo mashi Naira Miliyan Ɗari 100 da baburan da akafi sani da Boko Haram guda Goma 10 ba.

A hirar shi da Muryar Amurka, ta wayar tarho daga daji inda ya ke tsare da daliban 17 bayan kashe 5 daga ciki, Baleri ya ce ranar talata zai dau mummunan matakin matukar ba a turo sakon ba.

Baleri wanda ke nanata cewa da gaske ya ke yi wajen barazanar, ya bayyana cewa yanzu haka akwai mata 15 da maza biyu a hannun su da su ka hada da jikan marigayi sarkin Zazzau Shehu Idris mai suna Hamza.

Yayin da Baleri ke cewa iyayen yaran sun turo mu su diyyar da ta kai Naira Miliyan 45, ya ce sun sassauto daga wajen Naira miliyan 600 da su ka nema tun farko, yanzu su na bukatar miliyan 100 kuma sun yi amfani da kudin da a ka fara turowa wajen sayawa yaran garin ƙwaki.

Madugun barayi Baleri ya ce wannan shi ne wa’adi na ƙarshe da zai bayar na yau Litinin din nan.

Gwamnatin Kaduna dai na cigaba da nanata cewa babu batun biyan kudin fansa ga ƴan Ta’adda a faɗin jihar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here