Advert
Home Sashen Hausa A aikace, tsakanin Bahaushe, Bayarabe da Inyamuri wa yafi so a raba...

A aikace, tsakanin Bahaushe, Bayarabe da Inyamuri wa yafi so a raba Nigeria ne? ………..Daga Bala Anas babinlata

Duba da yadda Inyamurai suke kasa saka jari a kasar da suke kira kasarsu ya sanya min kokwanton anya da gaske suke yi suna son kafa kasar tasu? Idan ka dubi yadda suka hada karfi da karfe a musamman Lagos da Abuja da Kano. Suka zuba jari na trillions yayin da zai yi wuya ka samu Inyamurin da ya sanya jarin sama da miliyan dari zuwa dari biyu a kasar da yake kira Kasarsa, saboda fargabar makomar kasar ya sanya ina shakkar idan Inyamuri da gaske yake yi maganar neman ‘yanci. Idan da gaske suke yi me yasa suka tafi suke ta raya wasu bangarori na kasar da ba bangarensu ba. Gaskiya akwai wasan kwaikwayo a cikin lamarin.

Shi kuma Bayarabe ya fi kowa morar Najeriya, Ya fi kowa yawa a ma’aikatan tarrayar Najeriya, ya fi kowa yawan kamfuna da sana’o’i. Idan aka ce a ware wa zasu sayarwa da kayan da suke sarrafawa? Idan aka yi kasar Yarbawa hatta gabar teku dake kawo musu mahaukatan kudi na shipping sai ta girgiza. Don kuwa za a barsu ne da tsiyarsu kowa ya nemi mafita.

Malam Bahaushe bai furta da baki yana so a rabe ba, amma duba da halin ko’in kula dinsa ga kasar, kamar shi ya fi kowane dan Najeriya yin shakulatin bangaro da kasancewar Najeriya din a matsayin kasa daya. Kafin zuwan Usman Danfodio Bahaushe bai yarda da kasa ba, kowa garinsa shi ne kasarsa. Har yanzu Bahaushe bai sauya ba. In da za a ce a koma gidan jiya kowacce jiha ta koma matsayinta na asali gaskiya da Bahaushe zai fi so. Idan aka ce a dawo da Trans-Sahara-Route babu abin da zai dami Bahaushe. Idan ka ga Bahaushen dake son Najeriya ta cigaba da zama a matsayin kasa daya to tsirarin ‘yan siyasa ne da manyan masu mukamai da suke tatsar kasar kamar hauka. Idan muka dauke masu kudi irin Dangwate da Abdussamadu da suka yi karfi a wasu bangare na kasar nan. Bahaushe ya fi so ya zuba jarinsa a kasar hausa.

Duba da wannan hujjojin, ni a hangena Bahaushe yafi kowane Dan Najeriya son a raba Najeriya, a aikace ba wai a zance da hayagaga ba
Bala Ana’s shahararen marubuci ne a duniyar hausa.kuma darakta ne a fina finan hausa.

KATSINA CITY NEWShttps://www.katsinacitynews.com
Danjuma Katsina, Dan Jarida, Manazarci, Marubuci, Mamallakin Jaridun KATSINA CITY NEWS, JARIDAR TASKAR LABARAI, THE LINKS NEWS, a karkashin Kamfanin MATASA MEDIA LINKS NIGERIAN LTD

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

Yansanda A Katsina Sun Chika Hannu Da Yan Kungiyar Asiri Biyu

Rundunar Yan Sanda Ta Jihar Katsina ta kame wasu matasa biyu da make zargin yan Kungiyar Asiri ne. Kamar yadda Jami'in Hulda da Jama'a na...

WATA SABUWA: Kotu a jihar Gombe ta ci saurayi tarar Miliyan 2.6 saboda yaki auren budurwar sa

Daga: Yushau Garba Shanga Wata kotun majistiret da ke da zama a Kumo fadar ƙaramar hukumar Akko a jihar Gombe ta yanke wa wani matashi...

Rundunar Yansanda Ta Jihar Katsina Ta Chafke Daya Daga Cikin Yan Bindiga Da Suka Hallaka Hakimin Yantumaki.

Rundunar Yansanda ta Jihar Katsina ta samu nasarar chafke daya daga cikin Yan Bindiga da suka hallaka Tsohon Hakimin Yantumaki Marigayi Abubakar Atiku Maidabino,mai...

THE DUALIZATION OF THE IBADAN – ILORIN EXPRESSWAY AND SECTION II OF THE OYO – OGBOMOSO ROAD BY THE BUHARI ADMINISTRATION IS ALMOST DONE!

#PositiveFactsNG In staying true to its passionate commitment to developing Nigeria's infrastructure, do you know that the dualization of the Ibadan - Ilorin Expressway as...

THE APAPA – OSHODI – OWORONSHOKI EXPRESSWAY IS SET FOR COMPLETION AND COMMISSIONING!

https://www.facebook.com/Do-You-Know-NG-101788642037662/ THE APAPA - OSHODI - OWORONSHOKI EXPRESSWAY IS SET FOR COMPLETION AND COMMISSIONING! #PositiveFactsNG Do you know that the reconstruction project of the Apapa - Oshodi...