A ƙoƙarin Neman Hoton Kakana saida na tara Hotuna sunkai 2,500… -MT Safana-

Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Khadijah Abubakar @Katsina City News

Muhammad Tukur Ibrahim Safana (M.T Archives)

……..akwai Hoto guda ɗaya da na biya mashi Fan 70, a kuɗin Najeriya kusan dubu hamsin

.………Mun haɗa fiye da Mutum dubu Talatin, da suka gane danginsu a dalilin Hotuna.

Muhammad Tukur Ibrahim Safana, da akafi sani da M.T SAFANA ARCHIVES, da ya shahara wajen Nemowa da yaɗa tsaffin Hotunan Tarihi, a Ƙasar Hausa, a Firarsa da Katsina City News, ya sheda mana Dalilin sa na Fara yaɗa waɗannan Hotuna a kafafen Sada zumunta.

MT Safana, Shine Shugaban Hukumar Taimakekeniyar Lafiya ta Jihar katsina a karkashin Hukumar Inshorar Lafiya ta Najeriya, wanda yayi Digirin sa na biyu a ƙasar Seychelles, yace: “A dalilin Neman Hoton Kakana Sarki Abubakar saida na tara Hotuna, 1,700 na Tarihi, kuma ko wane da Asalinsa da bayanin sa, wasu ina biyan kuɗi masu yawa don in mallaki Hoton, akwai wani Hoto da na biya fiye da Dubu Hamsin a Kudin Najeriya sana na sameshi, kuma akwai Ire-iren su da dama, saboda wata Labirarin Ko ma’adanar Hotuna, suna Cajina kudi ne duk wata, amma Hoton da na fara Aikin domin sa ban sameshi ba.

MT Safana, yace bayan ya tara wadannan Hotuna, sai yaga babu buƙatar ya rabu dasu, duk da bai cimma gurinsa ba na gano Hoton Sarkin Katsina Abubakar, zai yi amfani da damar sa, na yaɗa waɗannan Hotuna, domin Al’uma su Amfana, sanin wadannan Hotuna shi kansa Ilimi ne, Inji Safana.

MT ya Shedama Katsina City News, Irin Nasarorin da ya samu, ta Dalilin wannan Aiki da Babu wanda ya sanyashi, Inda ya hada fiye da Mutum dubu talatin, suka fahimci juna suka gane su zuri’a daya ne, musamman Katsinawa mazauna wasu jihohi ko ƙasashe. Yace Masarautar Gwandu ta naɗashi Sarautar Bebejin Kalgo, sakamakon Hoton Wani sarki Basharu da suke nema wanda bai samu Hoton shi ba, sai ya samu na Mahaifinsa wato Sarki Halluru Abdu. da ya kaimasu jin dadin haka yasa suka naɗashi Sarautar.

Munada Cikkiyar Firar na Bidiyo. Ku tarba a kafar mu ta YOUTUBE: Katsina City News TV da Shafin mu na yanar gizo www.katsinacitynews.com

Ko a Twitter: @Katsina City News

Muna da Online Radio 📻 Instagram, Facebook page da Telegerem, zaku ji ku ga Dukkanin Shirye-shiryen mu da Shafukan mu, idan kuka sauke Application din mu, ta Playstor a wayoyin ku. Don Karin bayani: 07043777779, 07020570059

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here