Advert

… MABUƊIN ILIMI (8)

Yanda muka zagaye Jihar Katsina domin tattara Muhimman bayanan Tarihi da Hotuna.

Zaharaddeen Mziag @Katsina City News

KAITA L.G

A ranar 31 ga watan Mayu, muka isa ƙasar Kaita a cikin Masarautar katsina, babu inda mukayi pakin da Motar mu sai a Fadar Sarkin Sulluɓawan Katsina Hakimin ƙasar Kaita, mun isa fadar da wuri saboda da wuri muka taso daga cikin birnin Katsina.

Bayan mun isa mun samu tarba daga mutanen waje, kuma suka shedamana Sulluɓawan bayanan saidai wakilinsa, mukasa akayimana Iso wajen Wakilin Hakimi, amma mun ɗan samu jinkiri saboda mun iske ana wata shari’ar Aure tsakanin Mata da Miji (Shari’a me ban tausayi da ban Dariya) “kada ku tambayeni ya akai naji inda shari’ar ta sa gaba? Kunsan mun fito bin diddiƙi da ganin kwaf ne, kuma ba’a raba ɗan Jarida da neman labari” ba labarin shari’ar zanbaku ba muna akan labarin tafiyarmu Binciken tarihin jihar Katsina ne.

Bayan Wakilin Hakimi ya sallami masu Ƙara, mu kuma muka shiga. “Gaskiya angirmama mu” Kuma anji daɗin zuwan mu, munsha Tarihi na ƙasar kaita, daga bakin Wakilin Hakimi, daga nan muka wuce zuwa inda mukaga zahirin abinda suka bamu labari, mukayi Hotuna. Daga nan duk acikin ƙaramar hukumar Kaita nuka dau hanya zuwa garin Dankama, inda muka sadu da Sarkin Fulanin Dankma bayan maraba, sarki ya hadamu da Dan’uwan Mahaifinsa Dattijo Dan Boko Masanin Tarihin Alh. Ishaƙa Sarkin Fulani dankama, lallai Bawon Allahn nan ya karrama mu ya girmama mu, munsha lemu da nama kafin mu fara shan Tarihi (Allah ya sakama Alh. Ishaƙa Sarkin Fulani da Alheri) bayan mun kimtsa cikin mu, Alh. Ishaƙa ya shigo muka kunna na’urar naɗar Magana inda muka kwashi tarihin abunda bamu taba zata ba.

Zakuji abinda mukaji kuma zakuga abinda muka gani ta kafar sadarwar mu a www.katsinacitynews.com da Bidiyo a KATSINA CITY NEWS TV a YouTube channel din mu

Ko ku sauke Manhajar mu ta Application a Play Store ta wayoyin hannun ku.

Daga nan kuma sai ina?

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

NAF begins inquiry into alleged killings of civilians by Airforce pilot

The Nigerian Airforce has begun investigations into the alleged killing of civilians in Kamadougou Yobe State by an Airforce pilot. In a statement on Friday...

Yanzu haka cikin daren nan ‘yan bindiga sun afkawa garin Tangaza

LABARAI DA DUMI-DUMIN SU! Yanzu haka cikin daren nan 'yan bindiga sun afkawa garin Tangaza Labarai da muke samu sun tabbatar da cewa yanzu haka cikin...

Siyasa: PDP tayi watsi da tsagin Aminu Wali ta rungumi Kwankwaso

Siyasa: PDP tayi watsi da tsagin Aminu Wali ta rungumi Kwankwaso Babbar jam'iyyar adawa ta PDP ta sanya ranar gudanar da zaben sabbin shugabanninta na...

Abdulaziz Ganduje ya kai karar mahaifiyarsa Gwaggo EFCC kan batun almundahana

Babban dan Gwamnan Kano, Abdulaziz Ganduje ya maka mahaifiyarsa Hafsat Ganduje gaban hukumar yakibda yiwa tattalin arziki zagon kasa ta EFCC akan zargin da...

Barawon Motar Gwamnati Ya Shiga Hannu A Katsina

Barawon Motar Gwamnati Ya Shiga Hannu A Katsina. Rundunar Yan Sanda ta Jihar Katsina ta samu nasarar chafke wani mai suna Hayatu Bishir da ake...
%d bloggers like this: