Yan bindiga sun kai hari Makarantar Sojoji ta NDA

Bayanai daga jihar Kaduna da ke arewa maso yammacin Najeriya sun nuna cewa wasu ‘yan bindiga sun kai hari Makarantar Sojoji ta Nigeria Defence Academy, NDA, da ke birnin Kaduna.

Wasu mazauna gidajen da ke NDA sun tabbatar wa BBC Hausa cewa ‘yan bindigar sun kashe sojoji biyu sannan suka sace guda daya.

Sanarwar da mai magana da yawun Makarantar Sojojin Bashir Muhammad Jajira ya fitar ta tabbatar da kai harin.

Ya ce ‘yan bindigar sun shiga bangaren gidaje na Makarantar inda suka kai hari lamarin da ya yi sanadin mutuwar jami’ansu biyu sannan aka sace guda daya.

Amma bai bayyana mutanen da aka kashe ba, da kuma wanda aka sace. Sai dai wasu bayanai da BBC Hausa ta samu sun tabbatar da cewa an kashe “Lt Cdr Wulah da Flt Lt CM Okoronwo” sannan aka sace Manjo Datong.

“Al’ummar NDA da ‘yan makarantar horas da sojoji suna cikin koshin lafiya a Makarantar. Muna tabbatar wa jama’a cewa za a kamo wadannan ‘yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba nan gaba kadan sannan a ceto jami’an da aka sace,” a cewar Bashir Muhammad Jajira

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here