Advert
Home History Yanda muka zagaye jihar Katsina domin tattara Muhimman bayanai game da wuraren...

Yanda muka zagaye jihar Katsina domin tattara Muhimman bayanai game da wuraren tarihi da Hotuna (4)

… MABUƊIN ILIMI (4)

Yanda muka zagaye jihar Katsina domin tattara Muhimman bayanai game da wuraren tarihi da Hotuna (4)

ZANGO L.G(Masarautar Alh. Muhammad Hafiz Adamu) 

Zaharaddeen Mziag @Katsina City News 

Bayan Mun baro Babban Mutum ba tare da Biro yaga takarda ba, sai muka yada Zango, a Masarautar Zango (Zango L.G) duk a ƙarƙashin Masarautar Daura ta jihar Katsina. Da isar mu Kofar Fada, muka samu wuri muka yi Fakin da Mota, muka fito kai tsaye muka yi Sallama, wani da ke kwance yana ɗan rage gajiya a fadar ya farka daga Baccin da yake.

Bamu so tadashi ba, amma dole ta sa, sabida ba muga kowa wajen ba bayan ya tashi, muka bashi hakuri kuma muka gabatar da kan mu.

Nan take ya wartsake daga Bacci yayi mana Sannu da zuwa cikin Raha, da farinciki, yace;

“Kunzo a daidai, lallai kayan Tarihi tabbas akwai su, don ma zamani yazo ya tafi da waɗansu”

Da yake munje Dai-dai ana Sallar La’asar, sai muka gabatar da Sallah. Bayan kammalawa; wakilan Hakimin Zango, Usman Sani (Zangon Fada) me Unguwar garin Zango, da Abdullahi Sani (Galadima) Dukkansu Jikokin Hakimin Zango Murka Adamu, suka jagoranci gwada mana wuraren tarihi na ƙasar Zango da ƙaburburan Sarakunan Masarautar Zango, da Husainar Rijiyar Kusugu, me shekaru Aru-aru.

Suka shigar damu gidan Sarautar Zango, lungu da saƙo na gidan, dakuma bayani akan ko wane, abin Tarihi da suka gwadamana.

Bayan mun gama ziyarar dubawa da rubutawa na kayan tarihi a masarautar Zango daga nan sai ina?

Munada Hotuna da bayanan Wajajen Tarihi na Masarautar Zango, a Katsina City News

www.katsinacitynews.com

Ko Bidiyo na Kayan Tarihi a tashar mu ta Youtube me suna; KATSINA CITY NEWS TV

Ko ku sauke Manhajar mu ta Katsina City News a wayoyin ku ta Play Store.Tel: 07043777779

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

Shugaba Buhari ya nemi kasashen duniya su yafewa Najeriya bashin da suke binta

A yayin da yake gabatar da jawabi a zauren majalisar dinkin duniya a ranar Juma'a. Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nemi manyan kasashen duniya...

Bangaren aikin jarida na H.U.K Poly sun yaye kwararrin ‘yan social media a Katsina

Bangaren aikin jarida na H.U.K Poly sun yaye kwararrin ‘yan social media a Katsina Saifullahi Kuraye‎ September 24, 2021 2 min read Bangaren aikin jarida na...

Hukumar Hana Fasa ƙwabri ta ƙasa wato Custom ta ƙwato Babura Ɗari Biyu da Biyu a Jihar Katsina…

Shugaban Hukumar Ƙwastam na Jihar Katsina Mr. Chedi ne ya bayyana hakan ne a Yau Juma'a cewa tsakanin watan Agusta zuwa Satumba Hukumar ta...

Dan Najeriya ya fiye tsogwami: da ₦500 kacal sai aci a ƙoshi……Inji farfesa Segun Ajibola

Da Naira Dari Biyar ( 500 ) kacal Zaka Iyaci Ka Koshi a Najeriya, Cewar Wani Farfesa, Masanin Tattalin arziki... Tsohon shugaban kwalejin ma'aikatan bankin...

Rail project will not displace host communities-FG

Radio Nigeria The Federal Ministry of Transport and that of Environment have given assurance to residents along the proposed stretch of land demarcated for the...
%d bloggers like this: