Abin da ake nufi da ficewar Najeriya daga masassarar tattalin arziki

Shinkafa

Wasu ƙwararru sun ce fitar Nijeriya daga masassarar tattalin arziƙi a ƙarshen shekarar da ta wuce wani haske ne cewa ƙasar na kan hanyar samun bunƙasar arziƙi mai ɗorewa.

Sun ce hakan ya faru ne sakamakon ƙoƙarin gwamnati na haɓaka fannonin da ba na man fetur ba.

A jiya Alhamis ne wani rahoton Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasar NBS ya ce Nijeriya ta samu bunƙasar kashi 0.11 cikin 100 a tsakanin watan Oktoba zuwa na Disamban 2020.

Wannan na nuna cewa ƙasar ta fita daga karayar tattalin arziƙin da ta afka cikin Yuli zuwa Satumba.

Video content

Video caption: Ku saurari rahoton Mukhtari Adamu Bawa idan kuka latsa hoton sama

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here