Buhari ya amince da ɗaurin wata shida kan mutanen da ke ƙin sanya takunkumi

Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya sanya hannu kan dokar hukunta masu kauracewa bin dokokin kare kai daga kamuwa da korona.

Shugaban kwamitin da ke yaƙi da annobar kuma sakataren gwamnati, Boss Mustapha, ya tabbatar da hakan a Abuja, ya kuma ce an bijiro da dokar ne la’akari da yada mutane ke karya ka’idoji taƙaita yaɗuwar annobar.

Waɗanda hukunci ya hau kansu su hada da masu ƙin sanya takunkumi, wanke hannu, bai wa juna tazara da shafa sinadarin tsaftace hannu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here