Matar Sheikh Ibrahim El-Zakzaky ta kamu da korona a gidan yarin Kaduna

.

Mai ɗakin Sheikh Ibrahim EL-Zakzaky, Zeenat El-Zakzaky ta kamu da cutar korona, kamar yadda Malam Ibrahim Musa  ya tabbatar wa BBC.

A ranar Alhamis ne dai Sayyid Ibrahim Zakzaky, wanda shi ne ɗa namiji kaɗai da ya rage ga malamin, ya wallafa saƙo a shafin Twitter, inda ya bayyana cewa “kwanaki shida da suka gabata bayan likitocin da ke duba mahaifana sun ziyarce su a gidan yarin Kaduna, mahaifiyata sai ta yi ƙorafin cewa tana jin kasala da masassara haka kuma ba ta iya tantance tsakanin ƙamshi da wari”, in ji shi.

Ya bayyana cewa hakan ya sa aka yi mata gwaje-gwaje ciki har da na korona, inda gwajin korona da aka yi mata ya tabbatar ta kamu.

Sayyid dai ya yi ƙorafi matuƙa a saƙon da ya wallafa inda ya ce har yanzu mahaifiyarsa ba a kai ta asibiti ba kuma ba a ba ta kulawa ta musamman ba game da halin da take ciki.

Sai dai har yanzu gwamnatin jihar Kaduna ba ta ce komai ba kan wannan lamari da kuma batun ɓullar cutar korona a gidan yarin jihar.

Social embed from twitter

NO COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here