Yau laraba chikin ikon Allah maigirma tsohon Dan majalisar tarayya Wanda ya wakilchi karamar hukumar katsina Hon. Sani Danlami Mairaba Alkhairi, ya sayi form din tsayawa takarar kujerar majaliasar tarayya domin wakiltar Al’ummar karamar hukumar katsina a majalisar tarayya dake Abuja.

Masoya da dabam dabam sun halarci gidan shi dake unguwar modoji cikin garin katsina domin taya shi murna tare da fatan Alkhairi agare shi,

Daga karshe yayi godiya ga waɗanda suka samu Halartar gidan nashi yayi kira da jan hankali ga mutane kan su dage da addu’ar ga jahar katsina da kuma kasa baki daya inda yace yana amfani da Wannan damar ga domin ya kara mika sakon barka da Sallah da fatan Allah ya amshi ibadun mu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here