SAKON MAI NEMAN TIKITIN TAKARAR GWAMNAN JIHAR KATSINA ALH. UMAR ABDULLAHI TSAURI (UMAR TATA) ZUWA GA MAGOYA BAYANSA!

” Inshaa Allahu ranar talata 3 ga watan Mayu watau talata ta bayan sallah zani kaddamar da takara ta ga exco na ward dina da exco na local government a APC office na Dutsinma local government. Ba yan nan zamu kai ziyarar girmamawa ga stakeholders na APC na Dutsinma local government a karkashin jagorancin Hon Commissioner of Commerce don girmamawa da neman tubarki.

Ranar litinin 9 ga wata ko laraba 11 ga wata, duk wacce state HQ suka zaba zamu kai ziyara ta kaddamar da takarar mu a party headquarter ta jiha inshaa Allahu. Daga party office zamu wuce zuwa babban filin taro na kaddamar da takarar ga al’ummar jiha baki dayan ta don isar da sako ga al’ummar jihar Katsina ga baki daya.”

Sanarwa;
Office of the State Chairman,
Tata Media Campaign 2023,
Katsina State.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here