Gwamnan Jihar Sokoto kuma mai neman tsaya wa takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Aminu Tambuwal, ya yi watsi da yiwuwar cimma maslaha tsakanin masu neman takarar.

Wannan watsi da Tambuwal ya yi, ya zo ne ƙasa da mako ɗaya, bayan da ya yi iƙirarin cewa fitar da ɗan takarar shugaban kasa ta maslaha alheri ne ga PDP.

Sai dai kuma, Tambuwal ɗin ya yi mi’ara-koma-baya yayin da ya ke mayar da martani ga labarin da ke cewa gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed da tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki ne su ka fito a matsayin ƴan takara na maslaha a jam’iyyar.

“Hankalin Kungiyar Kamfe din Tambuwal (TCO) ya kai kan wani labari cewa tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki da Gwamna Bala Muhammad na jihar Bauchi sun fito a matsayin ‘yan takarar maslaha daga cikin mu hudu da mu ka bayyana a wani taro a Minna, Jihar Naija,” in ji sanarwar Nicholas Msheliza, daraktan kungiyar ta TCO.

“A gaskiya kuma a bayyane, ba gaskiya ba ne. Gaskiyar lamari shine, mun yi wata gana wa a ranar Laraba 20 ga Afrilu, 2022, a masaukin Gwamnan Bauchi da ke Abuja inda mu ka yi nazari a kan yanayin; kuma, gaba ɗaya mun yarda cewa tsarin maslaha ba zai yi aiki ba.

“Tawagar ta kuma amince da cewa Sanata Saraki ya fito da daftarin bayani kan yadda zai isar da wannan shawara ga al’ummar Najeriya. Wannan shine karo na ƙarshe da membobin ƙungiyar su ka zauna kuma su ka amince da juna akan wani batu. Amma sai gashi Saraki, ta kafar WhatsApp, ya yi gaban kan sa wajen rushe taron da a ka shirya yi na nazari da tantance bayanan da aka shirya gudanarwa da misalin karfe 10 na rana,” in ji Tambuwal.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here