2023: INEC ta yi wasu sauye-sauye a hedikwatarta

Hukumar Zaɓe Mai Cin Gashin Kan Ta ta Ƙasa (INEC) ta yi wasu sauye-sauye a hedikwatar ta a Sashen Ayyukan Shari’a da Sauraren Koke-koke (LSC &CC) da Sashen Wayar da Kan Masu Zaɓe da Yaɗa Labarai (VEP).

Wannan bayani ya na ƙunshe ne cikin sanarwar da Babban Kwamishina kuma Shugaban Kwamitin Yaɗa Labarai da Wayar da kan Masu Zaɓe na hukumar, Mista Festus Okoye, ya fitar a ranar Laraba.

Haka kuma ya bayyana cewa hukumar ta ƙirƙiro wasu sababbin ɓangarori guda biyu daga cikin Sashen Ayyukan Shari’a da Sauraren Koke-koke (LSC&CC) na yanzu.

Okoye ya ce sauye-sauyen sun zama dole ne a lokacin da hukumar ke shirin gudanar da muhimman zaɓuɓɓuka na gwamnoni da kuma babban zaɓen 2023.

Ya ce, “Hukumar Zaɓe Mai Cin Gashin Kan Ta ta Ƙasa (INEC) ta yi taro a yau, 22 ga Afrilu 2021, kuma daga cikin abubuwan da aka tattauna har da sauye-sauye da aka yi wa Sashen Shari’a da Sauraren Koke-koke (LSC&CC) da Sashen Wayar da Kan Masu Zaɓe da Yaɗa Labarai (VEP).

“A yayin da hukumar ke shirye-shiryen gudanar da muhimman zaɓuɓɓukan gwamnoni da babban zaɓen 2023, ya zama wajibi a sake yin nazari tare da saisaita wasu daga cikin sassan ta don tabbatar da ingancin aiki da kyakkyawan tsarin tafiyar da ma’aikata da kayan aiki.

“A saboda haka, hukumar ta ƙirƙiro sababbin sassa guda biyu daga cikin Sashen Shari’a da Sauraren Koke-koke (LSC&CC).

A sabon tsarin, an ƙirƙiri Sashen Ƙararraki (DL&P) da Sashen Rubuta Shari’a (LDCD).”

Kwamishinan ya ƙara da cewa hukumar ta amince da kafa Sashen Ilmantar da Masu Zaɓe, Yaɗa Labarai, Kula da Jinsi da Hulɗa da Ƙungiyoyin Jama’a (VEP) kuma a madadin ta an kafa Sashen Ilmantar da Masu Zaɓe da Yaɗa Labarai (VEP), da kuma Sashen Kula da Jinsi (GID).

A cewar sa, sauye-sauyen da aka yi Sashen Shari’a da Sauraren Koke-koke (LSC&CC) na gaugawa ne domin hukumar ta duƙufa wajen ƙarfafa ikon ta bisa doka na gurfanar da masu karya dokokin zaɓe a kotu.

Bugu da ƙari, Okoye ya nanata cewa hukumar ta kuma ƙudiri aniyar sanar da jama’ar Nijeriya dukkan tsare-tsaren ta kuma ta rungumi manyan ƙungiyoyin mata, naƙasassu da sauran jama’ar da ake warewa a harkokin zaɓe.

A cewar sa, waɗannan sauye-sauye da aka yi ba za su shafi tsari da aikin ofisoshin hukumar na jihohi ba.

Ya bada tabbacin cewa ofisoshin harkokin shari’a da sasanci na jihohi za su ci gaba da aikin su a ƙarƙashin Shugaban Sashen Ayyukan Shari’a, a yayin da Sashen Kula da Jinsi zai zama a ƙarƙashin Shugaban Sashen Ilmantar da Masu Zaɓe da Yaɗa Labarai.

Okoye ya nanata cewa sauye-sauyen za su fara aiki ne ba tare da ɓata lokaci ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here