‘Yan sanda sun dakile yunkurin kai hari kan matatar Dangote

Yan sanda a Najeriya sun sanar da dakile wani hari da wasu mutane suka yi kokarin kaiwa matatar tace man fetur na kamfanin Dangote dake birnin Lagos.

Wata sanarwar da kakakin ‘Yan Sanda Benjamin Hundeyin ya gabatar tace wasu mutane akalla 20 ne suka kutsa kai cikin kamfanin ta cikin teku da asubahin litinin, inda suka yi kokarin kwashe wasu kadarorin dake ciki, kafin daga bisani jami’an tsaro su tarwatsa su, RFI ta labarta.

Jami’in yace jami’an tsaro sun yi nasarar harbe mutum guda daga cikin barayin, kuma ya mutu lokacin da ake kokarin kai shi asibiti.

Hundeyin yace kwamishinan Yan Sandan Jihar Lagos Abiodun Alabi ya bada umurnin kara matakan tsaro a matatar.

Ku danna nan domin shiga shafin Jaridar mu kai tsaye don samun sabbin Labarai Da Dumi-Dumi 👉www.inuwarlabarai.com.ng

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here