Lokaci ya yi na sauya fasalin Najeriya – Nasir El-Rufai

Gwamna Nasir El-Rufai

Gwamna Nasir El-Rufai na Jihar Kaduna ya ce lokaci ya yi da ya kamata a sauya fasalin Najeriya domin bai wa jihohi ƙarin iko kan albarkatun ƙasa da ‘yan sanda.

Da yake magana a taron cika 50 da kafa Gidan Arewa a Kaduna ranar Asabar, El-Rufai ya ce sauya tsarin mulkin ƙasar na cikin abin da zai “kawo cigaban Najeriya”.

Gwamnan wanda ya bayar da misali da wani rahoton kwamitinsu na jam’iyyar APC a 2018 game da sauya fasalin Najeriya, ya ce akwai buƙatar a ƙara wa jihohi ƙarfin iko kan albarkatun ƙasa da sauran abubuwa.

Aikin kwamitin wanda APC mai mulkin Najeriya ta kafa a 2017 ƙarƙashin jagorancin El-Rufai shi ne, tsara yadda jam’iyyar ke kallon sauya fasalin ƙasa da zummar kowane ɗan Najeriya ya amfana daga cikakken tsarin jamhuriya, wanda Najeriya ke kai.

Daga cikin shwarwarin kwamitin, El-Rufai ya nuna cewa jihohi za su samu ƙarin iko kan albarkatun man fetur da gas da ma’adanai da gidajen yari da kuɗin haraji da yi wa kamfanoni rajista da sauransu.

Ya ce: “Ni ban san wata mazaɓa ba da ke adawa da manufar ƙara wa jihohi ƙarfin iko kan ma’adanai domin kyautata rayuwar waɗanda suke mulka.

“Hakan zai bai wa gwamnatocin jiha damar daina miƙa wa Gwamnatin Tarayya da shugaban ƙasa dukiya alhalin akasarin matsalolin da ‘yan ƙasa ke fuskanta za a iya magance su a matakin gwamnatin jiha.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

Ansako ɗaliban makarantar Kagara da aka sace

GSC Kagara: An sako mutum 41 da aka sace a makarantar Kagara ta Jihar Neja An sako ɗaliban makarantar Kagara da malamansu da ma'aikata guda...

PRESS RELEASE ; GANDUJE SACKS MEDIA AIDE

PRESS RELEASE GANDUJE SACKS MEDIA AIDE Governor Abdullahi Umar Ganduje of Kano state has relieved his Special Adviser on Media, Salihu Tanko Yakasai of his appointment...

KANO STATE POLICE COMMAND DIARY 26/02/2021

KANO STATE POLICE COMMAND DIARY 26/02/2021 7 DAYS ACHIEVEMENTS OF CP SAMA'ILA SHU'AIBU DIKKO, fsi IN KANO STATE ... As 9 Kidnapping Suspects, 8 Armed Robbery...

Bamu da Adalci, Dole ne mu cire batun Siyasa idan ba Haka ba Muna gidajenmu zamu Hallaka ~Inji Atiku Abubakar..

Bamu da Adalci, Dole ne mu cire batun Siyasa idan ba Haka ba Muna gidajenmu zamu Hallaka ~Inji Atiku Abubakar.. Tsohon mataimakin Shugaban Kasa Atiku...
%d bloggers like this: