Advert
Home Sashen Hausa TSAKANI NA DA GWAMNATIN KATSINA(1).....

TSAKANI NA DA GWAMNATIN KATSINA(1)…..

Daga Kabir Sadiq (Dan Abu)

A farkon shekarar 2016 na samu maigirma gwamna nace ina son ganinsa, ya gama ganawa da wasu mutane, ya kirani, bayan na gaishe shi, nace masa shawara ce nazo muyi, yace, “toh ina saurarenka”. Nace masa Your excellency makarantata wadda Saldefi ke haya kusa da Continental ina son in tada matar da ke haya wurin.

Mai girma gwamna yace “saboda me?” Nace masa ina son In yi amfani da wurin ne, ina son in yi Private College of Health Science and Technology a wurin, domin mu na da bukatar irin wadannan makarantun, Abba Sayyadi ya yi Cherish a Batsari, kuma akwai Islamic Community College of Health a Funtua, amma nan bamu da ko daya.

Kuma a lokacin na gaya ma maigirma gwamna abinda ake biyana kudin haya naira milyan Goma sha biyu (12m) a shekara.

Maigirma gwamna yace “ah wannan magana naji dadinta sosai”, kuma ya kara da cewa, “Alh. Kabir irin ku mu keso domin aciyar da Katsina gaba. Kuma yace mani “Alhaji Haruna Dalhatu ya gaya mani ka gina wata makaranta Pyramid Schools can bakin tsohuwar kasuwa kuma ka bashi Director na makarantar”. Nace masa haka ne Your excellency.

Maigirma gwamna yace mani “naga akwai wani dan wuri tsakanin makarantar (ta kusa da Continental)da kwalta, ba nawa bane”? Nace masa ba nawa bane wasu ‘yan filayen shaguna ne, maigirma gwamna yace mani, “toh kaje ka gano masu wuraren sai mu canza musu wani wurin wanda ma yafi nasu kai kuma sai a baka wurin don ka samu wurin parking da wasu bukatun makarantar”. Nayi godiya nayi bankwana.

Masu haya wurin na basu notice, bayan sun tashi, naje wajen maigirma gwamna nace masa masu haya wurin sun tashi, kuma ina da bukatu biyu a wajenka, yace, “wane bukatu ne”? Nace masa ina da liabilities ka taimaka a biyani, kana kuma ina da wasu kujeru na yan makaranta da na kawo daga Chana idan zai yiyu idan gwamnati zata sayi kujerun yara ka taimaka a sayesu, kudinsu a lokacin yakai 44 million, domin bani son in sai dasu da guntu-guntu. Nace masa aikin gyaran makarantar nake son inyi da wadannan kudade, domin nagabya masa aikin wurin da equipments da kayan Laboratories zai ci about 90 million.

Maigirma gwamna yace, “in je in rubuto takardar neman a biyani liabilities dina, da kuma ta kujeru. Duka na rubuta nakai masa.

RASHIN SANI YAFI DARE DUHU
To ganin Mustafa Inuwa yana abokin yayana kuma nasan maganar za ta iya zuwa wajensa, sai na same shi gida nayi masa duk bayanin yadda muka yi da maigirma gwamna, kuma na ba shi copy na takardun dana rubuta ma gwamna na neman biyan liabilities da na neman a sayi kujerun dana kawo daga China. Ya karanta kuma ya ce babu matsala. Na bar masa copy na takardun muka yi bankwana.

A cikin wadannan lokutan, sai Alhaji Salisu Mamman Continental yaba gwamnati gudummuwar solar lights don a sanya boarding schools saboda yara su rika yin karatun dare ko babu wuta, da solar deep freezers domin akai asubitoci don as amu haryar ajiye jini da sauran bukatun asibitocin.

Mun gama bikin amsar kayan sai maigirma gwamna yace mani Alh Kabir kai kuma me zaka bamu, nan take nace masa your excellency zan bada kujeru irin wanda na kawo daga China guda dari biyu (Wanda kudinsu 5 million) akai su Family Support School don amfanin yara, kuma zan saya musu 10 seater bus don hidimar makarantar. Gwamna yayi godiya kuma ya kirawo Commissioner ta ilimi Late Professor Halimatu (Allah ya gafarta mata dukkanin kurakuranta ameen)
Yace mata ga Alh. Kabir nan ya bamu kujeru da mota, ku tafi ku tsara yadda zan zo in kaddamar da kayan.

Na samu Commissioner office ta kirawo perm sec da other directors mu kayi bayani, kuma suka rubuta ma gwamna takarda cewar na kawo sample na kujerun dana bada gudummuwa, kuma guda dari biyu ne, suna neman a bada rana wadda za a kira gwamna ya kaddamar dasu
Bayan sati biyu naje ministry don inji ranar da zan kawo kujerun nan da mota, aka ce har yanzu basu samu amsar takardar ba.

Wannan takarda sai da aka yi wata biyar gwamna bai ganta ba an badda ta a gidan gwamnati.

Wata rana Shugaban kasa yazo Katsina muna airport wajen tarbarsa sai gwamna ya kira ni yace mani, “toh kai ina kujerun da kace zaka bamu”, nace masa your excellency ai ranar da muka yi magana da kai wan shekare na kai sample wajen commissioner kuma a ranar suka rubuto maka takarda ta neman amincewarka akan ranar da za kayi launching na kujerun da mota. Nan take yace mani shi bai ga wata takarda ba. Amma yace in koma wajen commissioner.

Nasamu commissioner nayi mata bayani, hankalinta ya tashi, tasa aka kirawo perm sec da wasu directors tayi musu bayani. Daga nan Director works Nakano ya bada shawarar a rubuta wata takardar a kai ma maigirma gwamna hannu da hannu, kuma haka aka yi. Suna wurin gwamna director ya kirani yace gwamna sai fada ya keyi yana chewa mutane masu arziki sun zo zasu taimaka amma ana tayi musu zagon kasa. Aka fidda ranar da za a kaddamar da kujerun nan da mota, aka turo yan press, commissioner ta ilimi, perm sec na ilimi perm sec ta ma’aikatar mata ta sauran manyan ma’aikatan ma’aikatar ilimi da abokan arziki duk an taru ana jiran gwamna, tun karfe 11 na safe har karfe 4 na yamma babu labari.
Daga karshe aka aiko da sako cewar commissioner ta amshi kayan a madadin gwamna. Alhaji Salisu Continental duk
gaban shi aka yi wannan diminiyar.

Mu koma maganar makaranta, na tada masu haya na fara gyaran makaranta, wata rana muna fira da maigirma gwamna sai nace masa your excellency na fara gyaran makarantar nan, sai yace mani eh yagani, domin yaje duba wani aikin da aka yi na hanyar ruwa kusa da makarantar kuma yaga aikin kuma yace yaga aikin yayi kyau.

Bayan kwana biyu muna fira sai gwamna yace mani “Alhaji Kabir kace za kayi College of Health Science amma SGS yace mani kaje kace masa saida makarantar zaka yi”. Nace wa gwamna ni bance masa zan saida makaranta ba na dai gaya masa yadda mu kayi da kai kan zan tada matar dake haya wurin don inyi college of Health a wurin. Kuma na gaya masa nayi maka magana akan liabilities dina da kuma maganar kujerun da nake son a saya, kuma wannan bayanin nayi masa shi fiye da wata shidda da suka wuce. Nan dai muka gama fira mu kayi sallama.

Sauran bayanin zai zo Insha Allahu.
Mun ciro daga shafin Facebook

KATSINA CITY NEWShttps://www.katsinacitynews.com
Danjuma Katsina, Dan Jarida, Manazarci, Marubuci, Mamallakin Jaridun KATSINA CITY NEWS, JARIDAR TASKAR LABARAI, THE LINKS NEWS, a karkashin Kamfanin MATASA MEDIA LINKS NIGERIAN LTD

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

THE FEDERAL MORTGAGE BANK OF NIGERIA (FMBN) HAS MADE HISTORY UNDER THE BUHARI ADMINISTRATION!

#PositiveFactsNG Do you know that ever since the Federal Mortgage Bank of Nigeria (FMBN) was established about 25 years ago, its greatest record of achievement...

YANZU-YANZU | Jirgin ruwan Bagwai dake jihar Kano mai dauke da fasinjoji 40 Yayi hatsari

Jirgin ruwan wanda ya debo dalibai mata da maza daga garin Badau zuwa garin Bagwai a jahar Kano yayi hatsari a cikin ruwan Yanzu...

ALLAH SARKI: ALLAH KA RABA MU DA RANAR NADAMA

Danjuma katsina  @Katsina City News A shekarar 2000 na dawo Katsina da zama, bayan shekaru na gwagwarmaya da tsallake siratsai kala-kala. Bayan na dawo na tsara...

Yadda Kotu Ta Ruguza Zaɓen Bangaren Ganduje Na Jam’iyyar APC

Wata babbar kotun Abuja ta soke zaben shugabannin jam'iyyar APC bangaren gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje. Alkalin kotun Hamza Muazu ya haramta zaben da...

EFCC Charges Corps Members To Take CDS More Seriously

The Port Harcourt Zonal Commander of the EFCC, Assistant Commander of the EFCC, ACE Aliyu Naibi has called on members of the National Youth...