Advert
Home Sashen Hausa RIKICI TSAKANIN MAHDI SHEHU DA GIDAN REDIYON VISION FM KADUNA!

RIKICI TSAKANIN MAHDI SHEHU DA GIDAN REDIYON VISION FM KADUNA!

 

Musa Ibrahim daga Kaduna @Katsina City News

Wani rikici ya barke tsakanin malam mahadi shehu shugaban rukunin kamfanonin dialogue da kuma gidan rediyon vision FM dake Kaduna.
A ranar asabar 16/10/2021 mahadi shehu da rakiyar wasu matasa masu yawa suka je ginin gidan rediyon vision na Kaduna suka jibge wasu motoci suka kuma fara cire cire na wuta da ruwa.
Ganin haka, wani ma aikaci na gidan rediyon ya kuble kofar shiga ya kuma Kira yan sanda.
Yan sanda suka iso da kama duk Wanda suka samu ciki yayi wannan kutse har da mahadi shehu kansa.
Inda aka kai su baki daya a ofis din su na Kaduna don bin Bahasin al amarin.
Katsina city news tayi magana da daya daga cikin daraktocin gidan rediyon ya fada masu cewa , da zamu bude gidan rediyo a Kaduna, mahadi shehu ya bamu gini mu zauna kyauta.ya kuma ce har karshen rayuwarsa
Da mahadi na fada da gwamnatin katsina yayi niyyar mu kyale masa gidan rediyon, yayi abin da yaga dama,muka fada masa kaida bata ce haka ba.Amma ana iya saka duk wani labari ko shiri nasa da bai sabama ka i da ba.sai dai wannan matsayar bata yi masa dadi ba.
Daraktan yace,watannin baya sai mahadi shehu ya rubuto takarda cewa ya bamu wasu watanni mu tashi.zai yi amfani da gidan shi.
Mun bashi amsa cewar, watannin da ya bamu sunyi kadan.ya bamu shekara daya zamu Nemi wani wuri mu koma.ya kuma amince da hakan.
Kwatsam, sai ya sake rubuto wata takardar,cewa yana nan matsayarsa ta farko mu tashi cikin watannin da ya bayar.muka bashi amsa muna nan akan matsayar mu ta farko, shekara daya.
Shekarar bata cika ba,yazo yayi mana wannan kutse.wanda yanzu maganar na hannun yan sanda.
Katsina city news, mun yi magana da mahadi shehu, domin jin ta bakin shi.
Ya bayyana mana cewa shi bada vision FM yake fada ba,yana da matsala da mutum daya ne kuma darakta a kamfanin na vision FM.
Kodayake yace vision FM basu yi mashi adalci ana ci masa mutunci a ciki, sun ki bashi damar ya mayar da martani.
Yace ya taimaki vision FM na sayar masu da gidan rediyon da yayi niyyar kafawa a Kano.yace ya sayar masu da sauki kuma suka rika biyanshi da kudi kadan,Kadan.
Yace, ya kuma zo ya basu wurin da sukayi ofis kyauta a Kaduna. amma duk da haka, ba suyi mani adalci ba, a rikicina da gwamnatin katsina.
Mahadi ya tabbatar mana da yarjejeniyar farko.ta su tashi, cikin shekara daya.sai yace na chanza shawara ne,Dana naga cewa,a Ofis din basu saka na urar signal ta watsa shirye shirye ba.
Sai na sake rubuta masu na chanza matsayar shekara guda.
Mahadi shehu ya tabbatar mana da cewa shi ya jagoranci aka je ginin na vision FM.kuma har da shi yan sanda suka tarar a cikin ginin.
Ya kuma tabbatar mana yanzu maganar na gaban yan sanda suna gudanar da bincike.
Katsina city news
Www.katsinacitynews.com
Jaridar taskar labarai
Www.jaridartaskarlabarai.com
The links news
Www.thelinksnews.com
07043777779.

KATSINA CITY NEWShttps://www.katsinacitynews.com
Danjuma Katsina, Dan Jarida, Manazarci, Marubuci, Mamallakin Jaridun KATSINA CITY NEWS, JARIDAR TASKAR LABARAI, THE LINKS NEWS, a karkashin Kamfanin MATASA MEDIA LINKS NIGERIAN LTD

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

THE FEDERAL MORTGAGE BANK OF NIGERIA (FMBN) HAS MADE HISTORY UNDER THE BUHARI ADMINISTRATION!

#PositiveFactsNG Do you know that ever since the Federal Mortgage Bank of Nigeria (FMBN) was established about 25 years ago, its greatest record of achievement...

YANZU-YANZU | Jirgin ruwan Bagwai dake jihar Kano mai dauke da fasinjoji 40 Yayi hatsari

Jirgin ruwan wanda ya debo dalibai mata da maza daga garin Badau zuwa garin Bagwai a jahar Kano yayi hatsari a cikin ruwan Yanzu...

ALLAH SARKI: ALLAH KA RABA MU DA RANAR NADAMA

Danjuma katsina  @Katsina City News A shekarar 2000 na dawo Katsina da zama, bayan shekaru na gwagwarmaya da tsallake siratsai kala-kala. Bayan na dawo na tsara...

Yadda Kotu Ta Ruguza Zaɓen Bangaren Ganduje Na Jam’iyyar APC

Wata babbar kotun Abuja ta soke zaben shugabannin jam'iyyar APC bangaren gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje. Alkalin kotun Hamza Muazu ya haramta zaben da...

EFCC Charges Corps Members To Take CDS More Seriously

The Port Harcourt Zonal Commander of the EFCC, Assistant Commander of the EFCC, ACE Aliyu Naibi has called on members of the National Youth...