Home Sashen Hausa Joe biden ya yi kira ga Najeriya ta daina murƙushe masu zanga-zanga

Joe biden ya yi kira ga Najeriya ta daina murƙushe masu zanga-zanga

Joe biden ya yi kira ga Najeriya ta daina murƙushe masu zanga-zanga

Joe biden ya yi kira ga Najeriya ta daina murƙushe masu zanga-zanga

..

Ɗan takarar shugaban ƙasar Amurka Joe Biden, ya yi kira ga Shugaban Najeriya da kuma sojojin ƙasar da su daina amfani da ƙarfi wurin muƙushe masu zanga-zanga.

An dai kashe wasu da ke zanga-zangar Endsars a yammacin Talata a Legas da kuma raunata su inda ake zargin jami’an tsaro ne suka aikata hakan.

“Ina mika ta’aziyya ta ga waɗanda suka rasa masoyansu a wannan rikicin. Dole ne Amurka ta goyi bayan ‘yan Najeriya masu gudanar da zanga-zangar lumana domin kawo sauyi ga ‘yan sandan ƙasar da dimokraɗiyya da kuma cin hanci a ƙasar,” in ji wata sanarwa da Mista Biden ya fitar.

Gwamnatin Legas dai ta bayyana cewa aƙalla mutum 30 suka raunta a rikicin, sai dai sojojin ƙasar sun musanta zarginsu da ake yi na kai hari ga masu zanga-zangar.

NO COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

%d bloggers like this: