Ɗan Najeriya ne ya samar da rigakafin korona na Pfizer

Rigakafin korona da kamfanin Pfizer ya samar an bayyana cewa ɗan asalin Najeriya ne ya jagoranci samar da rigakafin a Amurka.

Ofishin jekadancin Amurka a Najeriya ya wallafa hoton likitan Dr Onyema Ogbuagbo a Twitter tare da cewa shi ya jagoranci samar da rigakafin korona na farko mai inganci a Amurka.

Onyema Farfesan magani ne da cuttuka masu yaɗuwa a Jami’ar Yale.

Ya yi digirinsa na farko a Jami’ar Calabar a 2003.

Social embed from twitter

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here