A daidai lokacin da Arewa ke ƙara dulmiya a hannun ‘yan bindiga, a Jihar Katsina wani gogarman masu garkuwa da mutane mai suna Usman Idris da aka fi sani da Ruga Kachallah, ya nemi a biya shi diyyar dukkan buhunan hatsin sa da jami’an ‘yan sanda su ka banka wa wuta, kafin a yi sulhu da shi.

Sai dai kuma Rundunar ‘Yan Sandan Katsina ta yi watsi da kalaman na sa, inda ta bayyana cewa sau huɗu ana sulhu da Ruga Kachallah, amma sai ya tayar da tubar sa.

Kachallah shi ne babban gogarman ‘yan bindigar da ka hana Ƙaramar Hukumar Safana zaman lafiya da kewayen ta a Jihar Katsina, kamar yadda PREMIUM TIMES ta tabbatar.

Mazauna yankunan sun shaida wa wannan jarida cewa akwai dandazon ‘yan bindigar da ke ƙarƙashin Ruga Kachallah, waɗanda sun fitini garuruwa da ƙauyukan yankin da garkuwa da satar shanu da dukiyoyi masu tarin yawa, gaba-gaɗi.

Sai dai kuma wannan jarida ta ji cewa Kachallah ya na sana’ar da ta sa ya ke da farin jini sosai a garuruwan da ke kewayen Safana.

Ya mallaki motocin haya sosai waɗanda ake yi masa jigila garuruwan yankin ana tara masa kuɗaɗe.

Wannan sana’a da Kachalla ke yi ta samar wa matasa da dama aikin yi a kewayen. Kuma su na hamdala sosai ga Kachallah.

Kachallah: Ɗan Bindiga Kamar Ɗan Sarki:

Mutanen karkarar Rulumbusawa, Yartsaku, Maƙera, Gimi da Chirena da ke cikin Ƙaramar Hukumar Safana a Jihar Katsina, sai sun nemi iznin Kachallah kafin su fita zuwa gonakin su.

A Arewacin Runka, gari na biyu wajen girma a Ƙaramar Hukumar Safana, can ma manoma sun miƙa wuya ga ‘Daular Kachallah’, gogarman ‘yan bindiga.

Kachallah Da Gwamnatin Katsina: Kar-Ta-San-Kar:

Ba kasar sauran ‘yan bindigar da ke ɓoye a cikin daji ba, shi Ruga Kachallah a cikin garin Gimi ya ke zaune da iyalin sa. Ya san kowa, kowa ya san shi.

Kwanan nan mazauna garin sun hana jami’an ‘yan sanda kama wani yaron sa, wani ɗan ta-kife, mai suna Gulbi.

An ce Kachallah na bai wa Gulbi shanun da ya sato, shi kuma ya na sayar masa.

Lokacin da mazauna garin su ka hana ‘yan sanda kama Gulbi, sun shaida wa Kwamandan Eriyar Safana, Dutsin-Ma, Ɗanmusa, Kurfi da Batsari, Aminu Umar-Daye cewa, ba za su bari a kama Gulbi ba, saboda idan aka kama shi, Kachalla cewa zai yi da haɗin bakin jama’a aka kama Gulbi, kuma a kan su zai huce haushin sa.

Haka dai Umar Daye ya haƙura ya janye ‘yan sandan.

Sai dai kuma a ranar 25 Ga Mayu, jami’an tsaro sun koma har gidan Kachalla, ba su same shi ba, amma sun banka wa gidan wuta, su ka ƙone masa buhunan kayan abinci. Sannan kuma su tafi da matan sa biyu.

Sai dai kuma ‘yan garin sun yi taron-dangi sun kashe wutar.

Daga nan fa Kachalla ya fusata, ya riƙa kama mutane, har sai da aka sakar masa mata biyu sannan ya saki wani malamin firamare da ya damƙe. Kuma ya ƙara ƙaimi sosai wajen kama mutane ya na yin garkuwa da su, ana biyan sa diyya.

Sulhun Da Bai Tsinana Komai Ba:

Cikin 2016 ne Riga Kachalla ya haɗa kai da wasu fitinannun ‘yan bindiga da su ka haɗa har da Abdullahi Karki, wani tubabben ɗan bindiga a yanzu, su ka yi alƙawarin ajiye makamai a wani ƙwarya-ƙwaryan bikin karɓar tubar su a ƙarƙashin Sakataren Gwamnatin Jihar Katsina, Mustapha Inuwa. An yi bikin a ƙauyen Illela, cikin Ƙaramar Hukumar Safana.

Sai dai kuma ba a daɗe da yin sulhun ba, sai dakarun Kachalla su ka koma bakin aikin kama mutane, su na yin garkuwa da su, ana biyan Kachalla kuɗaɗen fansa.

Bayan jami’an tsaro sun matsa lamba, wani dakaren Kachalla mai suna Jummah Tambai, ya kwashe iyalin sa ya koma Jihar Nassarawa, daga can kuma aka ce ya koma wani wurin da ake haƙar ma’adinai a cikin dajin Jihar Osun.

Haka shi ma mahaifin Kachalla da ke zaune a ƙauyen Sulluɓawa cikin Ƙaramar Hukumar Safana, ya yi hijira ya koma garin Banki cikin Ƙaramar Hukumar Anchau, saboda ya kasa hana ɗan sa Kachalla ci gaba da fashi, hare-hare da garkuwa da mutane.

Wanda Ya Saba Da Lale Miliyoyin Kuɗin Fansa, Ba Ya Son Bari Saboda Gudun Talauci – Na-Ammee, Tubabben Ɗan Bindiga:

A tattaunawar PREMIUM TIMES Hausa da wani tubabben ɗan bindiga mai suna Na-Ammee, wanda abokin Kachalla ne, ya ce ya yi ƙoƙarin shawartar Kachalla ya daina kai hare-hare, domin hana manoma zuwa gona zai haifar da tsadar abinci, kuma ya na ƙuntata wa mutanen yankin mahaifar sa.

“Da wahala mutanen da su ka saba da lale miliyoyin kuɗaɗen fansa su na ƙirgawa, su dawo irin rayuwar su ta fama da rashi.

“Yanzu ni ɗin nan da na tuba na daina, yanzu haka ina tunanin na sayar da tsohon babur ɗi na domin na samu kuɗin noma gonaki na.” Inji Na-Ammee.

Abin Da Ya Sa Na Ke Garkuwa Da Mutane -Kachalla:

PREMIUM TIMES ta samu tattaunawa da Gogarman Daji Kachalla ta wayar tarho, inda ya amsa laifin hare-haren da ake cewa ya na kaiwa.

“Ni da duk abin da aka gaya maka ina yi, ko ka ji ana cewa na yi, to duk ma aikata. Amma ina yi ne saboda dalili.

“Jami’an tsaro sun kama yara na huɗu da mata na biyu, kuma su ka ƙona min hatsi har buhu 100.”

Kachalla ya ce idan ana so ya daina, tunda an saki matan sa, to a saki sauran yaran sa huɗu, kuma a biya shi diyyar buhunan hatsin sa 100 da ‘yan sanda su ka banka wa wuta. Ya ce kowane buhu ɗaya ya tashi a kan naira 30,000.

“Saboda buhuna 160 na noma. Bayan na fidda zakka lokacin Ramadan, na yi saura buhu 100, wanda Area Kwamanda na ‘Yan Sandan Dutsin-Ma ya zo su ka banka wa wuta, kuma ya kama mata na biyu.

“A lokacin na kira lambar wayar Area Kwamanda ɗin, amma bai ɗaga ba, saboda ya san abin da ya yi min. Kuma na kira Hakimin Safana da Shugaban Ƙaramar Hukumar Safana duk na sanar da su, amma ba su yi komai ba.”

“Da na ga sun ƙi sakin matan, ni kuma sai na kama wani malamin makaranta, na ƙi sakin sa, har sai da aka saki matan nawa su biyu tukunna.

“Amma dai har yanzu ina neman a biya ni diyyar hatsi na buhu 100 da aka ƙone ƙurmus.” Inji Kachalla.

“Raina Min Wayau Aka Yi A Wurin Sulhu, Shi Ya Sa Na Tayar Da Tuba” -Kachalla:

“Ina cikin waɗanda aka yi zaman sulhu da su a Katsina. Amma sai ba a kula da ni yadda ya kamata ba. Aka damƙa min wani akwalar babur, su kuma wasu da su ka tuba din aka yi masu hidimar da ta fi wadda aka yi min yawa. To ka dai ji dalilin tada tubar da na yi” Inji Kachalla.

Kakakin ‘Yan Sandan Katsina, Gambo Isa ya ce ba za su amince da sharuɗɗan da Kachalla ya gindaya ba.

“Saboda sau huɗu ana yin sulhu da shi, amma ya na tada tuba.

Majiya: Premium Times Hausa

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here