Advert
Home Sashen Hausa Ɓullar Kwalara a Katsina; Ɗaliban Sheikh Zakzaky na ɓangaren kula da Lafiya...

Ɓullar Kwalara a Katsina; Ɗaliban Sheikh Zakzaky na ɓangaren kula da Lafiya sun ja Hankalin Gwamnati da Al’uma…

Zaharaddeen Ishaq Abubakar @Katsina City News

ISMA na ɓangaren Harkar Musulunci ƙarƙashin jagorancin Sheikh Zakzaky dake garin Katsina, sunja Hankalin Gwamnati da Al’uma akan ɓullar cutar Kwalara (Amai da gudawa) Inda sukayi kira ga Al’umar jihar katsina da su sanya ido sosai gami da Tsaftace muhallai zuwa abinci ko abin sha,

Sun bayyana wasu daga cikin alamomi, da suke bayyana ga masu ɗauke da cutar wanda idan aka ga sun bayyana ayi gaggawar ɗaukar matakai da suka dace.

Daga cikin alamomin da ake gane mutum ya kamu da cutar, shine Amai babu ƙyaƙƙyautawa, gami da Gudawa mai kamada dafaffiyar shinka, daga cikin matakan kariya shine saurin sanar da Hukumomin da abin ya shafa, don gudun yaɗuwar cutar, rage ziyarar mai ɗauke da cutar, shan magunguna da ƙarin Ruwa, (Kuma ana rigakafi).

A bangaren Gwamnati; ISMA sunyi kira ga Hukumomi jami’an tsaro, na ko wane ɓangare da su taru su taranma cutar domin ganin bayanta, gwamnati, ta tallafa da magunguna, inda suka bada misali da tsadar ledar karin Ruwa (Drop) wanda kuɗinta a yanzu da cutar ta ɓulla ya kai ₦1000 saɓanin da da bata wuce 200 zuwa 300, inda abin ke neman gagarar mai ƙaramin karfi.

Sunyi wannan kiran ne a Muhallin zaman juyayin Kisan Imam Hussain (Ashura) na shekara-shekara da suke gudanarwa a Irin wannan wata na Al’muharram, a gidan Sheikh Yaqub Yahaya bayan kammala karatun Ashurar.

A ƙarshe Sheikh Yaqub Yahaya dake jagorantar Zaman a Katsina ya bada addu’a da za’adunga karantawa domin neman kariya daga Annobar kamar haka;

اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَآِلِهِ الطَّاهِرِينَ

بِسْمِ اللهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيمِ

اللَّهُمَّ إِنَّكَ عَلِيمٌ حَلِيمٌ ذُو أَنَاةٍ , وَ لَا طَاقَةَ لَنَا بِحُكُمِكَ يَا اللهُ يَا اللهُ يَا اللَّــــــهُ , اَلْأَمَانَ اَلْأَمَانَ اَلْأَمَانَ مِنَ الطَّاعُونِ وَ اَلْوَبَاءِ وَ مَوْتِ اِلْفُجْأَةِ, وَ سُوءِ اِلْقَضَاءِ وَ شَمَاتَةِ اِلْأَعْدَاءِ , رَبَّنَا اَكْشِفْ عَنَّا اَلْعَذَابَ إِنَّا مُؤْمِنُونَ إنَا مُوقِنُونَ بِرَحْمَتِكَ يَا أَرْحَمَ الرَّاحِمِينَ, وَصَلَّى اللهُ عَلَى مُحَمَّدٍ وَآِلِهِ الطَّاهِرِينَ.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

Shugaba Buhari ya nemi kasashen duniya su yafewa Najeriya bashin da suke binta

A yayin da yake gabatar da jawabi a zauren majalisar dinkin duniya a ranar Juma'a. Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nemi manyan kasashen duniya...

Bangaren aikin jarida na H.U.K Poly sun yaye kwararrin ‘yan social media a Katsina

Bangaren aikin jarida na H.U.K Poly sun yaye kwararrin ‘yan social media a Katsina Saifullahi Kuraye‎ September 24, 2021 2 min read Bangaren aikin jarida na...

Hukumar Hana Fasa ƙwabri ta ƙasa wato Custom ta ƙwato Babura Ɗari Biyu da Biyu a Jihar Katsina…

Shugaban Hukumar Ƙwastam na Jihar Katsina Mr. Chedi ne ya bayyana hakan ne a Yau Juma'a cewa tsakanin watan Agusta zuwa Satumba Hukumar ta...

Dan Najeriya ya fiye tsogwami: da ₦500 kacal sai aci a ƙoshi……Inji farfesa Segun Ajibola

Da Naira Dari Biyar ( 500 ) kacal Zaka Iyaci Ka Koshi a Najeriya, Cewar Wani Farfesa, Masanin Tattalin arziki... Tsohon shugaban kwalejin ma'aikatan bankin...

Rail project will not displace host communities-FG

Radio Nigeria The Federal Ministry of Transport and that of Environment have given assurance to residents along the proposed stretch of land demarcated for the...
%d bloggers like this: