Ɓatanci ga Annabi a Kano: An ci gaba da shari’ar mutumin da ya yi ɓatanci ga Manzon Allah

An example of hangman's noose

Wata babbar kotun jihar Kano da ke Najeriya ta soma sauraren ƙarar da mutumin da aka samu da laifin yin kalaman ɓatanci ga Annabi Muhammad S.A.W. ya ɗaukaka.

A watan Agusta ne wata kotun Musulunci da ke jihar ta yanke wa wani matashi mai shekara 22, Yahaya Aminu Sharif, hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa yin ɓatanci ga manzon Allah.

Ta same shi da laifin yin kalaman na ɓatanci a cikin wata waƙa da ya yi a watan Maris na 2020.

A gefe guda, kotun ta yanke wa wani matashin mai suna Umar Farouq hukuncin kisa shi ma bisa laifin ɓatanci ga Allah Maɗaukakin Sarki.

Ya yi ɓatancin ne yayin da suke yin ce-ku-ce da wani, a cewar masu shigar da ƙara.

Sai dai dukkansu sun dauƙaƙa ƙara zuwa babbar kotun da ke jihar ta Kano.

Abin da ya faru a Kotun

An soma shari’ar ce ranar Alhamis ƙarƙashin jagoranci alƙalai biyu – Babban alƙalin Kano, mai shari’a Nura Sagir Umar da kuma mai shari’a Nasiru Saminu.

Lauyan Aminu Shariff, Barista Kola Alapinne, ya ƙalubalanci hukuncin kisan da kotun shari’ar Musulunci ta yanke masa yana mai cewa hakan ya saɓa wa kundin tsarin mulkin Najeriya.

Ya nemi kotu ta yi watsi da hukuncin kotun shari’ar Musuluncin.

A game da shari’ar Umar Farouq, Barista Kola Alapinne, wanda shi ne lauyansa, ya nemi kotun ta yi watsi da hukuncin.

Ya buƙaci kotun ta sallami mutanen biyu.

Sai da lauyar da ke wakiltar gwamnatin Kano, Barista Aisha Mahmoud, ta yi kira ga kotun ta tabbatar da hukuncin da kotun Musulunci ta yanke a kan mutanen.

A nasu ɓangaren, alƙalan kotun sun ce nan gaba za a kira lauyoyin ɓangarorin biyu a sanar da su ranar da za a yanke hukunci kan ƙararrakin.

Zanga-zangar Allah-wadai

Protesters
Tun a watan Maris ne matasa suka yi sun yi zanga-zangar neman a hukunta wani Yahaya Sharif-Aminu, wanda suka zarga da yi wa Annabi Muhammad S.A.W batanci.

Matasan sun yi cincirundo ne a gaban ofishin hukumar Hisbah, inda kwamandan hukumar ya tarbe su.

Kafin lokacin, wasu fusatattun matasa suka far wa gidan mahaifan mawakin a unguwar Sharifai da ke kwaryar birnin Kano tare da lalata abin da ke ciki.

Hukuncin zai zama izina ga sauran jama’a

Kotu

“Wannan hukuncin zai zama darasi ga sauran jama’a wadanda ke ganin za su ci mutuncin addininmu da ma’aikin Allah ba tare da an dauki mataki ba,” in ji shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here