Daga Abdul’razak Ahmad Jibia.
A daren jiya Asabar Bakwai ga watan Mayun 2022, ƴan ta’adda ɗauke da muggan makamai suka zagaye garin Jibia ta Jihar Katsina, suna yunƙurin shiga domin su yaƙi Al’ummar garin.
Wani mazaunin ƙauyen “‘Gurbin Magarya”‘ mai suna Halliru Haladu ya shaida mana cewa miyagun sun yi nasarar shiga kauyensu inda suka kashe tare da raunata wasu magidanta da matasan kauyen, kimanin Mutane Ukku sun rasa rayukan su, An kuma raunata Ukku da harbin bindiga, kazalika kuma sun ƙwashe dabbobi marassa adadi, a yayin wannan harin.
A cewar mazaunin ƙauyen hakan ya faru ne a yayin da wasu ke neman mafaka, wasu na gudun tsira, wasu kuma na yunƙurin kare kansu da ga harin Ƴan ta’addar ta martabarsu da ta iyalansu.
Haladu, ya kuma kara da cewa tun a tsakar daren da abin ya faru ne aka garzaya da waɗanda suka jikkata zuwa Babban Asibitin garin Jibia, inda likitoci suke ci gaba da kula da lafiyarsu.
Majiyar dai ta sunayen Mutanen da suka rasa Rayukan su da ma waɗanda suka jiggata sun haɗa da; Muntari Naqawuri, Sirajo Salisu, da Musa Hassan a matsayin waɗanda suka rasa rayukan su, Sai kuma Mustafa Salisu, Basiru Abubakar, da Muhammad Rabi’u (Babba) a matsayin waɗanda suka jiggata.
Wasu daga cikin mazauna ƙauyen na ‘”Gurbin Magarya”‘ sun bayyana rashin kawo ɗaukin gaggawa daga Jami’an tsaro, a matsayin babban abinda yasa Ƴan ta’addar suka yi nasara, Amma kuma sun tabbatar da mana da cewa, wata motar Jami’an tsaro ta kai ɗauki bayan da Ƴan bindigar suka arche.