Ƴan bindiga sun kashe kansu a wani ba-ta-kashi a dajin Katsina

Bindiga

An yi ba-ta-kashi tsakanin ɓangarori biyu na ƴan bindiga a kauyen Illela da ke karamar hukumar Safana ta Katsina, lamarin da ya yi sanadin rayuka da dama baya ga wadanda suka jikkata.

Rikicin ya kaure ne tsakanin ɓangaren Mani Sarki da kuma Dankarami a sansanin Abu Rada, a cewar jaridar Daily Trust.

Majiyoyi sun shaida cewa rikicin ya biyo bayan nadama da Sarki ya yi da kuma amincewa da afuwar gwamnati lamarin da ya sa ake masa kallon barazana da tafka rikici a kansa a sansanonin da ke dazukan yankin.

Rahotanni sun ce amincewa da wannan afuwa ya sanya Sarki sauya mazauni domin sake sabuwar rayuwa, amma hakan ya tunzura wasu daga cikin mukarrabai da yaran da ya ke aiki da su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here