Ɓarayi 5 sun haɗu da ajalinsu a hannun wasu matasa a Kaduna, an ƙona biyu ƙurmus

Wasu fusatattun matasa a Kaduna sun kashe ɓarayi biyar a Ƙananan Hukumomin Sanga da Lere, kamar yadda kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar, Samuel Aruwan ya tabbatar.
Tun da farko dai, biyu daga cikin ɓarayin sun kai wa wani ɗan kasuwa hari inda suka ƙwace masa kuɗaɗe a Fadan Karshi da ke Sanga.
Sai dai ko da jami’an tsaro suka isa inda lamarin ya faru sai suka tarar da wasu fusatattun matasa sun ƙona ɓarayin ƙurmus.
Kwamishinan ya ƙara da cewa a Ƙaramar Hukumar ta Sanga dai, wasu ‘yan bindiga sun ɓude wa motoci wuta kan hanyar Aboro zuwa Kafanchan.
A yayin da suke harbin, sai harsashi ya sami wani mai suna Richard Sabo wanda ya kaɗe ɗaya daga cikin ɓarayin da mota bayan motar ta ƙwace masa.
A Ƙaramar Hukumar Lere kuma wasu matasa ne da suka shahara wurin satar dabbobi su ma suka haɗu da ajalinsu a wurin fusatattun matasa.
Kwamishinan ya bayyana cewa an bi ɓarayin su uku inda aka ci ƙarfinsu a ƙauyen Domawa, inda a nan ne matasan suka kashe su.
A cewar kwamishinan, Gwamnan jihar, Nasir El-Rufai ya ja hankalin matasan jihar da su guji ɗaukar doka a hannunsu.