Ƙoƙarin da Hukumar Zaɓe ta Ƙasa, INEC ta shafe shekaru ta na yi, don ganin Majalisa ta kafa dokar aika sakamakon zaɓe ta yanar gizo, ya ci tura ne yayin da ‘Yan Majalisar Tarayya da ta Dattawa akasari ‘yan ɓangaren APC su ka ƙi amincewa da ƙudirin dokar.

Wannan ƙudiri dai INEC ta so ya zama doka, domin yin hakan zai magance hanyoyin maguɗi sosai a lokutan zaɓuka a ƙasar nan, tun daga zaɓen 2023.

Yayin da Majlisa ta baɗa wa INEC ƙasa a ido, su ma jama’a da dama sun taya INEC alhini da jimamin wannan rashin nasara da hukumar zaɓen ta yi.

A ranar 15 Ga Yuli, Majalisar Tarayya ta ƙi amincewa da ƙudirin, maimakon haka, sai ta tura ƙudirin a hannun Hukumar Sadarwa ta Ƙasa (NCC), domin ta duba yiwuwar aika sakonnin sakamakon zaɓe ta yanar gizo.

Sai dai kuma PREMIUM TIMES ta gano cewa Hukumar NCC ta yi ƙunbiya-ƙumbiyar ƙin faɗa wa Majalisa gaskiya.

Wannan jarida ta gano cewa akwai yarjejeniya da aka ƙalla tun a cikin 2018 cewa hukumomin biyu sun amince za a iya aika sakamakon zaɓe ta yanar gizo a lokacin zaɓen 2019.

Abin mamaki shi ne yadda ita hukumar NCC ɗin ta ce babu isasshen ƙarfin intanet a kusan rabin rumfunan zaɓukan ƙasar nan, don haka ba za a iya aika saƙonnin sakamakon zaɓe ta yanar gizo ba. Alhali kuma tun a 2018 hukumar ta shaida wa INEC cewa abin zai yiwu a zaɓen 2019.

Babu Wadatar Ƙarfin Intanet A Rabin Rundunar Zaɓen Ƙasar nan -Inji NCC:

PREMIUM TIMES Hausa ta buga labarin yadda Hukumar NCC ta ce kashi 50% na rumfunan zaɓen ƙasar nan ba su da intanet mai ƙarfin tura sakamakon zaɓe.

Kwana ɗaya bayan da Majalisar Dattawa ta bayyana cewa ta miƙa batun amincewa da ƙudirin aikawa da saƙonnin sakamakon zaɓe ya yanar gizo ga Hukumar Sadarwa ta Ƙasa (NCC), hukumar ta ce yin hakan ba zai yiwu ba, domin kashi 50% cikin 100% na rumfunan zaɓen ƙasar nan duk ba su da ƙarfin intanet wadda za ta iya aikawa da sakamakon zaɓe ta yanar gizo.

Babban Jami’in NCC Ubale Maska ne ya bayyana halin da ya ce rumfunan zaɓen ke ciki na rashin ƙarfin intanet.

Maska ya yi bayanin a gaban Majalisar Tarayya yayin da aka gayyaci NCC ta yi bayanin shin ko tura sakamakon zaɓe ta yanar gizo.

An gayyace shi ne biyo bayan hatsaniyar da ka kaure a Majalisa, tsakanin masu goyon bayan yin amfani da yanar gizo a tura sakamakon zaɓe da waɗanda ba su goyon baya.

Maska ya ce cikin 2018 Hukumar NCC ta yi binciken gwaji a rumfunan zaɓe 119,000 a yankuna daban-daban na ƙasar nan.

“Mun gano cewa kashi 50% kaɗai a cikin su ke da ƙarfin intanet mai nauyin 3G wanda zai iya aika sakamakon zaɓe ta yanar gizo. Saura kashi 46.7 duk mai nauyin 2G gare su. Sauran rumfunan kuwa kwata-kwata babu.

“Ya kamata a sani cewa 2G ba ya iya aika sakamakon zaɓe ta yanar gizo, sai 3G.” Inji Maska.

Tuni dai ‘yan Najeriya ke ta yin tofin tir ga ‘Yan Majalisar Dattawa da na Tarayya waɗanda ba su goyi bayan yin amfani da aika sakamakon zaɓe ta yanar gizo ba.

“Ya za a ce ka cika fam ɗin neman aiki ta yanar gizo, ka aika kuɗi ta yanar gizo, a cika fam ɗin N-Power a yanar gizo, a yi rajistar NIN a yanar gizo, a cika fasfo a yanar gizo, a biya haraji a yanar gizo kuma a yi wa lambar waya rajista da yanar gizo, sannan a ce ba za a iya tura sakamakon zaɓe ta yanar gizo ba? Wannan dai maguɗi kawai ake so a yi a 2023.” Inji Ibrahim Sani a Kano.

INEC Ta Ƙaryata NCC, Ta Ce Aika Sakamakon Zaɓe Ta Yanar Gizo Zai Yiwu:

A lokacin da Majalisa ta maida lamarin a hannun NCC, ta gayyaci jami’an INEC da kuma na Hukumar NCC domin ƙarin bayani.

Sai dai kuma INEC ta cika da fushi, ganin cewa bayan jami’in NCC Ubale Maska ya yi bayanin cewa aika sakamakon zaɓe ta yanar gizo ba zai yiwu ba, Majalisa ba ta bai wa jami’an INEC damar yin magana ba.

Wannan lamari ya kai ga Daraktan Yaɗa Labarai na INEC, Nick Dazang garzayawa Gidan Talbijin na AIT inda aka yi hira da shi a Shirin Kaakaki, ya ƙaryata Hukumar NCC.

Dazang ya bayyana cewa akwai matsayar da INEC da NCC su ka cimma tun a cikin 2018 cewa zai yiwu a aika a saƙonnin sakamakon zaɓe ta yanar gizo a zaɓen 2019.

“Shin wanda ya yarda cewa hakan zai yiwu tun a 2018, ya kuma a cikin 2021 zai zo ya ce hakan ba zai yiwu a zaɓen 2023 ba?

Dazang ya ƙara da cewa akwai kwafi na yarjejeniya ko matsayar da INEC ta cimma tare da NCC a rubuce tun a 2018, kafin a yi zaɓen 2019.

“Dalilan NCC ba abin yarda ba ne. Nan fa Hukumar Jarabawar JAMB ta haɗa hannu da kamfanonin MTN da Airtel, aka riƙa tura sakamakon jarabawa ta yanar gizo. To ya za a ce kuma tura sakamakon zaɓe ta yanar gizo ba zai yiwu ba?” Inji Dazang.

Ya ce INEC ta tanadi na’urori da manhajojin da za su hana ‘yan dandatsa kutsawa cikin rariyar manhajar tattara sakamakon zaɓe idan an amince da bin tsarin.

Majiya Premium: Times Hausa

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here