A yau Lahadi Honarabul Hajia Zainab Suwuɗi ta bar Jam’iyyar PDP ta koma NNPP inda Shugaban Jam’iyyar na Katsina Alhaji Sani Liti Ƴan Kwani ya amshe su a Offishin Jam’iyyar na Katsina
A lokacin Gabatar da jawabin nata Hon. Haj. Zainab Suwiɗi tace daliln da yasa ta dawo wannan jam’iyyar shine ganin yadda Engr. Nura Khalil ya dawo cikin Jam’iyyar ta kara da cewa Engr. Nura Khalil ya kware wajen Taimakon marayu da masu karamin karfi da kuma irin yadda yake ba da Gudunmuwar shi fanni daban daban
Ta kara da cewa lalle zasu bada Gudunmuwar su wajen ganin ansamu nasara cikin ikon Allah
Shugaban Jam’iyyar Hon. Sani Liti Ƴan Kwani Yayi masu Maraba da shugowa Jam’iyya Mai Albarka ta NNPP kuma ya yaba ganin yadda tururuwar mata suka zo wurin inda yace insha Allah nasara tamu ce kuma idan Allah ya bamu wannan mulki zamu kamanta adalci cikin ikon Allah
Shugabar mata ta Jam’iyyar da saura shugaban sunyi yabo da sambarka ga tawagar baki daya.