Rundunar Ƴan Sandan Jihar Katsina, Karkashin Jagorancin Kwamishinan Ƴan Sanda, Alhaji Sanusi Buba Ta Yi Nasarar Kama Wani Hatsabibin Mai Safarar Makamai Dan Shekara Arba’in Da Biyar, Sani Mamuda Dan Asalin Garin Shama Dake Karamar Hukumar Birnin Magajin Jihar Zamfara.

Mai Magana Da Yawun Rundunar, SP Gambo Isa Ya Bayyana Cewa An Kama Shi A Karamar Hukumar Kurfi Ta Jihar Katsina, Bayan Samun Bayanan Sirri Da Jami’an Rundunar Suka Samu Akansa.

An Samu Bindiga Kirar Ak49 Da Ak47 Da Harsasai Arba’in Da Biyu Da Kuɗin Najeriya Dana Jamhuriyar Nijar A Hannunsa Da Kuma Mashin Din Hawa Kirar Bajaj, Wanda A Cikinsa Yake Saƙa Bindigun.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here