Rundunar Ƴan Sandan Jihar Katsina, ta yi nasarar Matashi Ahmed Abdulmuminu Wanda aka fi sani da Khaleefa Sardauna, wanda ke zaune a Unguwar Shagari Low-cost, cikin garin Katsina bisa zargin cin zarafin jami’in gwamnati, Alhaji Ibrahim Umar wanda aka fi sani da Teacher Na Masari a shafin Sada Zumunta Na Facebook.

Kakakin rundunar, SP Gambo Isa ya bayyana haka ga manema labarai a helkwatar rundunar dake kan hanyar Daura, a cikin garin Katsina yau Talata.

SP Gambo Isa ya ci gaba da cewa “Abinda ya faru shi ne Alhaji Ibrahim Umar (Teacher Na Masari) ya yi bikin ranar zagayowar haihuwarsa , lokacin da ya ke bin shafinsa na Facebook domin duba waɗanda suka yi masa fatan alheri, ya ci karo da sakon da aka ci zarafinsa aka kuma keta masa haddi. Sai ya rubuta wa kwamishinan yan sanda, takardar korafi akan lallai abi masa hakkinsa kuma lokacin da muke gudanar da bincike, mun gano wanda ya aikata wannan laifi, watau Ahmed Abdulmuminu” Cewar Gambo Isa

Shima da ya ke bayani gaban manema labarai, Matashi Ahmed Abdulmuminu Aminu ya bayyana cewa an kawo ni bisa zargin da Iro Teacher Na Masari ke yi man na na ci mutuncinsa. Na yi rubuce-rubuce da yawa, wanda shi yake zargin da shi nike duk da ban kama sunan kowa ba, maganganu ne da yawa wadanda suke da alaƙa da siyasa.

Khalifah Sardauna ya kara da cewa wanda na yi , ba wanda ake zargina ba akai, na amsa na yin, na yi shi ne saboda abinda Iro Teacher ya yi man, akwai wani aiki da maigirma gwamna ya ba ni, ya ce in je in lissafa kuɗin aiki, in ba Teacher ya ba ni kuɗin aikin in je in yi aikin, bayan na kawo masa lissafi ya ce sai ya ga maigirma gwamna, kullum na yi masa magana ya ce sai ya ga maigirma gwamna, har ta kai ga lokacin aikin ya wuce, domin aiki ne da ke da alaƙa da yakin neman zaɓe na 2018-2019.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here