Ƴan sanda Najeriya na farautar ƴan bindigar da suka yi garkuwa da marayu

police

Ƴan sanda a Najeriya na farautar ƴan bindigar da suka kai hari wani gidan marayu tare da garkuwa da mutum shida, a birnin ƙasar na Abuja.

A ranar Asabar ƴan bindiga suka farwa gidan marayun da ke yankin Abaji a wajen garin Abuja, tare da garkuwa da yara ƴan shekaru 10 zuwa 13.

Sannan ƴan bindigar sun sace mazauna yankin mutum 3, kamar yada ƴan garin suka shaida, bayan jin harbin bindiga.

Ƴan sanda sun shaida wa BBC cewa an ceto yaro guda cikin 3 da aka sace.

Babu dai ƙarin haske amma ƴan sanda sun ce suna farautar ƴan bindigar domin ceto sauran yaran.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here