Yan Najeriya na Allah-wadai da kalaman Garba Shehu a hirarsa da BBC

Channels TV

‘Yan Najeriya, a shafukan sada zumunta, na yin Allah-wadai da kalaman Garba Shehu mai magana da yawun Shugaba Buhari game da kalaman da ya yi a hirarsa da sashen Ingilishi na BBC a safiyar Litinin.

Kakakin shugaban ƙasar na amsa tambaya ne kan ko manoma 43 da ake zargin Boko Haram da yi wa yankan rago a Borno sun samu amincewar jami’an tsaro kafin su yi noma a gonakin nasu.

Sai ya amsa da cewa: “A’a, wajibi ne a faɗi gaskiya. Shin sojoji da ke kula da yankin sun amince? Ko wani daga cikinsu ya nemi amincewa kafin ya ci gaba da aiki? Shugabannin sojoji sun faɗa mani cewa ba su nemi shawara ba, saboda haka wannan damar ‘yan ta’addan suka yi amfani da ita.”

Garba Shehu ya ƙara da cewa akasarin yankunan an ƙwace su ne daga hannun Boko Haram kuma akwai wurare da yawa da ba a amince mazaunansa su koma ba tukunna. “Ya kamata a ce sojoji sun amince tukunna kafin a ci gaba da ayyuka a yankunan.”

Mutane da dama a Twitter sun caccake shi kan waɗannan kalamai nasa, ciki har da waɗanda suka yi masa fatan ya mutu ta wannan hanya.

Aliyu ya ce: “An wanke ni, yau Garba Shehu ya kare kashe-kashen Zabarmari kuma babu abin da zai faru.”

Shi kuma Ayemojubar tambaya yake cewa “to saboda haka wannan ya zama hujjar kashe su kenan, dubi abin da fadar shugaban ƙasa ke faɗi”.

A martanin da ya mayar, Garba Shehu ya ce shi ma “mutum ne mai cike da tausayi da jinƙai, saboda haka ba zai taɓa cewa maonoman sun cancanci abin da aka yi musu ba saboda sun ƙi bin umarnin sojoji”.

Ya ce yana amsa tambaya ce kawai kan ko suna da lasisin ci gaba da ayyukansu a wurin ko kuma a’a, “kuma amsa ita ce babu”, in ji shi.

Ba Garba Shehu kaɗai bai, masu amfani da shafukan zumuntar sun nemi Buhari ya sauka daga kan mulki, suna masu zarginsa da gazawa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here