Advert
Home Sashen Hausa ƳAN FANSHO SUN YABA WA SHUGABA BUHARI BISA BIYAN SU KUƊAƊEN FANSHO...

ƳAN FANSHO SUN YABA WA SHUGABA BUHARI BISA BIYAN SU KUƊAƊEN FANSHO DA ARIYAS

Fassara: Hon. Buhari Sallau Hadimin Shugaban kasa Muhammadu Buhari Bangaren Rediyo da Talabijin.

Ƴan fansho a Najeriya karkashin Ƙungiyar Ƴan Fansho na Ƙasa, (Nigeria Union of Pensioners) sun rubuta wasikar Godiya da Jinjina ga Shugaba Muhammadu Buhari, kan biyan kaso Mafi tsoƙa na kuɗaɗen hakkin su da suke bin a baya.

Cikin wasikar wanda ke dauke da rattaba hannun Babban Magatakardan Ƙungiyar, Elder Actor Zal. Ƴan fanshon sun bayyana Buhari a Matsayin Shugaba “wanda ke sauraron da Nuna So da ƙyakƙyawar fata” ga wannan batun” ya nunar cewa hakan shaida ce ta “kokari da Gwamnatin sa tayi domin sanya fuskokin mebobin mu cikin annashuwa.”

Ga abinda wasikar ta ƙunsa nan biye:

“Shugabanni da duk daukacin membobin na Kungiyar Fansho, suna fatan bayyana farin ciki ga Mai girma Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari GCFR, dangane da bada iznin biyan hakkin Ƴan Fansho da samar da kuɗaɗen domin biyan cikin ƙanƙanin lokaci na kuɗaɗen ariyas na shekaru biyu.

“Duk da kalubalen da tattalin arziki ke ciki, daga lokacin da aka saki takardan iznin, Shugaban Kasa ta hanun Hukumar shirya biyan kuɗaɗen fensho suka fara biyan Ƴan Fansho da duk daukacin ƙasa, ta Gurin fara biyan na watanni Goma sha biyu, 12 wanda tuni aka fara a watan Shida, da kuma sake biyan watanni Shidda a cikin watan Bakwai, wanda ya rage watanni shida kawai ya rage. Muna fatan cewa za’a ka rasa biyan a lokacin daya dace.

“Ƙungiyar ta lura da irin gagarumin kokari da nuna damuwa da Gwamnatin ka tayi don sanya annashuwa a fuskokin membobin mu dake Ƙasa baki daya, ya zamo wajibi mu nuna godiya wa Gwamnatin ka.

“Wannan aikin da kayi kawai yana kara shaida gaskiyar cewa kai, babu shakka shugaba ne mai sauraron wanda ke bukatu.

“bamu da bakin maka Godiya

Femi Adesina:
Mashawar ci Na Musamman ga Shugaban Kasa a Fannin Yada Labaru da Wayar da kan Jama’a.
03 ga watan Ogusta , 2021

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

RESOLUTIONS OF THE NORTHERN STATES GOVERNORS’ FORUM MEETING WITH NORTHERN STATES EMIRS AND CHIEFS HELD ON MONDAY 27TH SEPTEMBER, 2021

The Northern States Governors’ Forum, in its continuous efforts to address the challenges bedeviling the Northern States convened an Emergency Meeting today Monday 27th...

Zaben Shuwagabannin Jam’iyyar APC a Katsina… Tsohon Ciyaman yasa mu kware Fostar Dan’takara:

Zaben Shuwagabannin Jam'iyyar APC a Katsina... Tsohon Ciyaman yasa mu kware Fostar Dan'takara: Zaharaddeen Ishaq Abubakar @Katsina City News An Ja Zare tsakanin masu neman kujerar...

ME KAMFANIN GREEN HOUSE YAKE BOYEWA NE? (1)

ME KAMFANIN GREEN HOUSE YAKE BOYEWA NE? (1) Sharhin jaridun Katsina City News Kamfanin da ke buga jaridun Katsina City News, jaridar Taskar Labarai da The...

BISA KUSKURE: Sojojin Najeriya sun sake kashe fararen hula 20

Sojojin Najeriya sun sake kashe fararen hula 20 a bisa ga kuskure Sojojin Najeriya sun sake kashe fararen hula 20 a bisaga kuskure a garin...

Zagayen Juyayin ‘Yan Shi’a: Jami’an tsaron Najeriya sun buɗe wuta a Abuja

Zagayen Juyayin 'Yan Shi'a: Jami'an tsaron Najeriya sun buɗe wuta a Abuja... Rahotanni dake shigomana daga Abuja nacewa, gamayyar Jami'an tsaro, na Najeriya sun buɗe...
%d bloggers like this: