Ƴan Bindigar Da Suka Sace Tsohan Shugaban Gidan Talabijin Na Jihar Katsina Da Diyarsa Sun Nemi A Ba Su Kuɗin Fansa Har Naira Miliyan 70

Yan bindigar da suka yi garkuwa da tsohan Manajan Gidan Talabijin Na Jihar Katsina kuma Tsohan Darakta a Hukumar Lura Da Gidajen Rediyo Da Talabijin Ta Kasa, Alhaji Ahmad Abdulkadir da diyarsa Laila Ahmad yar shekara goma sha biyar a gidansa dake rukunin gidaje na Shema a karamar hukumar Bakori ta jihar Katsina a ranar Litinin din da ta gabata, sun nemi tsabar kudi har Naira Miliyan 70.

Nasif Ahmad daya daga cikin ƴaƴansa, ya bayyana Majiyar Blueink News Hausa cewa yan bindigar sun kira ta wayar salula inda suka nemi a ba su zunzurutun kuɗi har naira Miliyan saba’in, inda suka ce Miliyan Hamsin ta mahaifin na mu, sai kuma miliyan ashirin ta Laila Ahmad yar shekara goma sha biyar, wadda suka bayyana cewa ta na fama da matsananciyar rashin lafiya, har ta kai ba ta iya tafiya.

Kakakin rundunar yan sanda ta jihar Katsina, SP Gambo Isa ya ce rundunar tana bakin kokarinta ganin ta kuɓutar da su cikin koshin lafiya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here