Wasu ƴan bindiga da a ke kyautata zaton ƴan kungiyar Masu Fafutukar kafa Ƙasar Biafra, IPOB ne, sun kai hari kan wata motar sintiri ta Sojoji a garin Aba, cibiyar kasuwancin Jihar Abia.

Jaridar The Nation ta jiyo cewa lamarin ya faru ne da sanyin safiyar Juma’a, lokacin da sojojin ke sintiri.

An kuma bayyana cewa maharan sun yi wa sojojin kwanton bauna ne.

Lamarin ya afku ne a babbar mahadar Tonimas a Ƙaramar Hukumar Osisioma, a kan titin Enugu-Aba-Port Harcourt.

Rahota Ni sun baiyana cewa maharan sun kuma kona motar sintirin sojojin.

Sai dai har yanzu ba a tantance adadin wadanda su ka mutu ba a harin.

Wata majiya daga cikin jami’an tsaro ta ce lamarin ya faru ne da misalin karfe uku na dare, inda lamarin ya haifar da fargaba da zama ɗar-ɗar da ga mazauna yankin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here