Bayanan da ke shigo ma Jaridar Blueink News Hausa na cewa yan bindigar da suka yi garkuwa da yayan sakataren gwamnatin jihar Katsina, dattijo dan shekara sama da saba’in, Alhaji Kabir Muhammad Burkai, wanda mahaifinsu daya da Sakataren Gwamnatin Jihar Katsina, Alhaji Mustapha Muhammad Inuwa ya kuɓuta daga hannun yan bindigar.

Majiyar Blueink News Hausa, ta shaida mata cewa sun sako shi da yammacin da yau Litinin, kuma ba a biya ko sisin kobo ba, bayan kwashe kwanaki shidda a hannun yan bindigar.

Da farko sun nemi a ba su Miliyan Hamsin har su ka dawo Miliyan goma, amma aka ki ba su, amma an kama wanda ya kwarmata masu su zo su sace shi, watau (Informer) da wasu daga cikin yan uwan wadanda suka je har gonarsa dake wani kauyen Daftau da rana suka sace shi domin biyan kuɗin fansa, wanda kuma suka sako ba tare da an biya kudin fansar ba.

Kabir Muhammad Inuwa dai tsohon jami’in dan sanda ne da ya yi ritaya da dadewa, babban manomi ne, kuma yana zaune ne da iyalan sa a garin na Danmusa ta jihar Katsina.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here