Ƴan Bindiga sun sake kai hari a jihar Kaduna tare da hallaka mutum tara..

Daga Shehi Falalu

Maharan da ba’a san ko su waye ba sun sake kai hari ƙauyen Makarau Jankasa dake ƙaramar hukumar Zangon Kataf, jihar Kaduna, inda suka kashe aƙalla mutum 9, Kamar Yadda Rahoton Jaridar Leadership ya nuna.

An bayyana Cewa Mafiyawan Mazauna ƙauyen Sunyi gudun hijira zuwa makwabtansu.

Idan Baku Manta ba Wannan harin yazo ne kwanaki uku kacal bayan wasu yan bindiga sun kai hari ƙauyen Warkan dake ƙaramar hukuma ɗaya da wannan, inda aka kashe mutum 9 tare da jikkata wasu da dama, kuma aka ƙona gidaje 12, Cewar Jaridar punch.

Mr. Donald Bityong, mazaunin ƙauyen ne ya tabbatar da kai harin ga manema labarai a yau Litinin.

Yace yan bindigan sun mamaye ƙauyen Makarau Jankasa jiya Lahadi da misalin ƙarfe 5:00 na yamma.

Ya ƙara da cewa jami’an tsaro sun kawo ɗauki ƙauyen ne lokacin yan ta’addan sun gama aikin ta’addancin su sun fice.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here