Ƴan Bindiga Sun Kone Gari Kurmus Da Marecen Yau Juma’a A Katsina

Ƴan bindiga dauke da makamai, sun kai hari a garin Yantuwaru dake gundumar Ruwan Godiya a karamar hukumar Faskari a jihar Katsina, inda suka kone gidajen garin da yammacin yau Juma’a.

Wani mazaunin garin Rabe Ahmed Ƴantuwaru ya shaidawa Blueink News Hausa ta waya cewa yan bindiga sun kai harin da yammacin yau.

Ahmed Rabe ya ce yan bindiga sun kaddamar da harin da marecen yau, bayan yan garin sun dawo daukar sauran kayayyakinsu, daman sun kore su daga Garin, inda suke zaune garin na su da dadewa, watau mun bar garin, da suka ji mun zo daukar kayan suka kawo hari inda suka kone gidajenmu baki daya.

Rabe Ahmed Ƴantuwaru ya cigaba da cewa yanzu haka Mutum guda ya bace da shi da iyalansa matansa ukku da yara. Yan bindiga nan suka gudanar da bukukuwan Sallah a garin na mu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here