Advert
Home Sashen Hausa Ƴan Bindiga Sun Kashe Mutum Biyar Da Kone Wasu Kone Wasu Gidaje...

Ƴan Bindiga Sun Kashe Mutum Biyar Da Kone Wasu Kone Wasu Gidaje A Kananan Hukumomin Musawa Da Matazu A Jihar Katsina

Yan bindiga dauke da bindigogi sun kai hari a wasu Kauyukan Kananan Hukumomin Musawa da Matazu inda suka kashe mutum biyar har lahira da sace dabbobi da dama da kuma kone wasu Kauyukan daga Alhamis zuwa daren jiya Asabar.

Majiyar Blueink News Hausa dake yankin ta shaida mata cewa yan bindigar sun kai harin a cikin karamar hukumar Musawa, a daren Juma’a inda suka kore dabbobi da dama, sun shiga garin da misalin karfe takwas da hamsin, sun kwashe tsawon awa guda cikinsa, amma ba su kashe kowa ba, sun dai saci dabbobi.

A daren Asabar, yan bindigar sun kai hari a kauyen Dugul dake gundumar Mazoji Yalwa Papu a karamar hukumar Matazu, inda suka kashe mutum huɗu, ciki har da Mai Unguwar garin, Malam Rabi’u. Sun kone gidaje da dama na garin tare da kwashe masu

Majiyar ta ci gaba da cewa sun kai makamanci harin a wani kauyen Gidan Mamman Dangata dake arewacin Musawa, suka yi musayar wuta tsakanin mutanen gari da yan bindigar, inda suka kashe mutum daya cikin yan gari da raunata mutum daya, su ma yan garin sun kashe dan bindiga guda har lahira, amma yan bindigar sun samu nasarar kore masu shanu masu shanu.

Majiyar Blueink News Hausa ta nakalto cewa daren jiya Asabar, yan bindigar sun kai hari a kauyen Ilali, dake cikin karamar hukumar Matazu, inda suka dira gidan wani mutum, Allah ya sa ya boye kan rufin gidansa da ya ji tahowarsu, sai suka rufe dakinsa suka banka wa dakin wuta, sanadiyyar hakan ya kone a wasu sassan jikinsa, yanzu haka yana kwance a babbar Asibitin garin Malumfashi yana jinyar konewar da ya samu.

Haka zalika, sun kashe mutum daya, tare da kone gidaje da dama, da kuma balle shagunan yan kasuwar garin da sace dabbobi masu dinbin yawa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

RESOLUTIONS OF THE NORTHERN STATES GOVERNORS’ FORUM MEETING WITH NORTHERN STATES EMIRS AND CHIEFS HELD ON MONDAY 27TH SEPTEMBER, 2021

The Northern States Governors’ Forum, in its continuous efforts to address the challenges bedeviling the Northern States convened an Emergency Meeting today Monday 27th...

Zaben Shuwagabannin Jam’iyyar APC a Katsina… Tsohon Ciyaman yasa mu kware Fostar Dan’takara:

Zaben Shuwagabannin Jam'iyyar APC a Katsina... Tsohon Ciyaman yasa mu kware Fostar Dan'takara: Zaharaddeen Ishaq Abubakar @Katsina City News An Ja Zare tsakanin masu neman kujerar...

ME KAMFANIN GREEN HOUSE YAKE BOYEWA NE? (1)

ME KAMFANIN GREEN HOUSE YAKE BOYEWA NE? (1) Sharhin jaridun Katsina City News Kamfanin da ke buga jaridun Katsina City News, jaridar Taskar Labarai da The...

BISA KUSKURE: Sojojin Najeriya sun sake kashe fararen hula 20

Sojojin Najeriya sun sake kashe fararen hula 20 a bisa ga kuskure Sojojin Najeriya sun sake kashe fararen hula 20 a bisaga kuskure a garin...

Zagayen Juyayin ‘Yan Shi’a: Jami’an tsaron Najeriya sun buɗe wuta a Abuja

Zagayen Juyayin 'Yan Shi'a: Jami'an tsaron Najeriya sun buɗe wuta a Abuja... Rahotanni dake shigomana daga Abuja nacewa, gamayyar Jami'an tsaro, na Najeriya sun buɗe...
%d bloggers like this: