Home Sashen Hausa Ƴan bindiga sun kashe mutum 8 da ƙona buhunan masara 330 a...

Ƴan bindiga sun kashe mutum 8 da ƙona buhunan masara 330 a Kaduna

Ƴan bindiga sun kashe mutum 8 da ƙona buhunan masara 330 a Kaduna

.

Rahotanni daga jihar Kaduna na cewa ƴan bindiga sun kai hari a kasuwar Galadimawa da ke Ƙaramar Hukumar Giwa, lamarin da ya ja aka tafka mummunar asara.

A wata sanarwa da kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar, Samuel Aruwan ya fitar, ya bayyana cewa ‘yan bindigar sun kashe ‘yan banga biyu da wasu mutum biyar.

A harin dai, ‘yan bindigar waɗanda suka je kasuwar kan babura 15 sun yi sanadiyar ƙonewar wata ƙaramar mota da kuma buhunan masara 330 da ke cikin wata tirela mallakar wani direba mai suna Alhaji Yusuf Tumburku.

Rahotanni dai sun ce ɓarayin tun farko sun shiga kasuwar ne da misalin ƙarfe huɗu na yamma inda suka buɗe wa ƴan bangar wuta.

Amma daga baya jami’an tsaro da suka haɗa da sojojin sama sun bi ɓarayin inda suka samu nasarar kashe wasu daga cikinsu, kamar yadda sanarwar da kwamishinan ya fitar ta bayyana.

NO COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

%d bloggers like this: