Bayanan da ke shigo ma Blueink News Hausa na cewa yan bindiga sun kai hari a daren jiya a kauyen Masaku da ke gundumar Gundawa a karamar hukumar Kankara, inda suka kashe mai Unguwar Garin, Malam Yahuza har lahira, sun kwashe dabbobi garin kaf a daren jiya Asabar.

Majiyar Blueink News Hausa ta shaida mata cewa ko satin da ya gabata sun kai hare-haren a kauyukan da dama a gundumar Bakam da ke karamar hukumar Musawa, inda suka fara tun daga kauyen Hayin Gidan Tambai sun dauke Mutum biyu daga nan suka wuce Damawa suka dauki yan mata biyu da sace dabbobi garuruwan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here