Ƙungiyar ci gaban Fulani, Kautal Hore ta baiyana cewa ta kammala shirye-shirye na kafa kasuwar sarrafa nonon shanu a Ƙaramar Hukumar Hadejia da ke Jihar Jigawa.

Shugaban ƙungiyar, reshen Jigawa, Alhaji Umar Dubantu ne ya shaidawa Kamfanin Daillancin Labarai, NAN a Dutse a yau Litinin.

Ya ce za a kafa kasuwar ne gami da haɗin gwiwa da gwamnatin jihar da kuma ƙaramar hukumar ta Hadejia.

A cewar sa, tuni ma a ka share filin da za a fara aikin kafa kasuwar.

Dubantu ya yi bayanin cewa idan a ka kafa kasuwar, za ta taimakawa mata masu kawo nono da ga Masarautar Hadejia, Katagum da Azare a Jihar Bauchi, har da ma Nguru a Jihar Yobe.

A cewar sa, ƙungiyar za ta zaɓo ta kuma tallafawa ƴan matan Fulani da firjina a wani tsari na adashin gata domin ya taimaka musu su riƙa ajiye nono a kasuwar.

Ya nuna cewa hakan zai sa masu sayar da nonon su riƙa samun rarar kuɗaɗe tun da ba sai sun koma da shi gida, kuma washegari su dawo kasuwa da shi ba.

Shugaban ya ƙara da cewa bayan samar da aikin yi ga matasa, kasuwar kuma za ta riƙa tarawa gwamnatin jihar kuɗaɗen shiga.

Ya kuma baiyana cewa za a tallafawa matasa Fulani guda 5 da bashin kuɗi domin su riƙa kawo man shanu kasuwar.

Daily Nigerian Hausa

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here