Yan bindiga: Ƙungiyar Arewa ta juyawa Gumi baya, ta ce ya je ya ƙwaci kansa

Daga Yahya Abdullahi Birnin Gwari

Kungiyar dattawan arewa ta nesanta kanta daga wasu kalaman Sheikh Gumi

– Ta kuma bayyana cewa ya zama dole kungiyoyin arewa su fito su yi watsi da wadannan kalamai nasa don kada a yi zaton su yake ciwa albasa

– Hakan ya biyo bayan furucin da Gumi yayi na ikirarin cewa ‘yan bindigar sun fusata saboda sojoji wadanda ba Musulmi ba ne ke kashe su

Kungiyar dattawan Arewa a ranar Laraba sun nesanta kansu daga maganganun kwanan nan da aka alakanta da malamin addinin Musulunci, Sheikh Abubakar Gumi, wanda ya zama jakadan sulhu da ’yan fashi a dazuzzukan da ke fadin jihohin Kaduna, Zamfara, Katsina , da Neja.

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa a yayin daya daga cikin irin wadannan tarurrukan, ya yi zargin cewa sojoji wadanda ba Musulmi ba sun aiwatar da kisan gilla a wasu garuruwa, lamarin da ya fusata su.

“Abin da nake so ku fahimta shi ne, sojojin da ke da hannu a cikin yawancin laifukan ba Musulmi ba ne. Ku sani, sojoji suna da musulmai kuma suna da wadanda ba musulmai ba.

Wadanda ba Musulmai ba ne ke haifar da rudani don kawai a haddasa rikici,” in ji Gumi.

Ya fadi hakan ne ga wata tawaga karkashin jagorancin Sakataren Gwamnatin Jihar Neja a kan aikin sulhu don sakin daliban Kagara da aka sace.

Amma dattawan da ke karkashin kungiyar Dattawan Arewa maso Gabas kan ci gaban Zaman Lafiya (NEEPD) sun ce zargin na Gumi bai wakilci matsayin yankin ba , suna masu cewa dole ne jama’a su yi wa abun kallo a matsayin “ra’ayin kansa”.

Yayinda take kira ga jama’a da suyi watsi da wannan zargi, kungiyar ta NEEPD a cikin wata sanarwa daga jagoranta, Zana Goni, ta sha alwashin yin watsi da duk wani yunkuri na mutum ko wata kungiya kan sojin.

A cewarsu, ya zama dole manyan kungiyoyin Arewa su yi Allah wadai da ikirarin Gumi mai hadari, don kada mutane suyi tunanin cewa yana magana ne da yawun yankin.

Duba ga kalaman nasa, ta iya yiwuwa Gumi na kare fashi da makami ne.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here