Ƙungiyar ƙwadago ta janye yajin aiki a Kaduna

BBC

Haɗaɗɗiyar ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa (NLC) janye yajin aikin da ta shiga a Jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya.

Nasir Kabir mai magana da yawun ƙungiyar, shi ne ya tabbatar wa da BBC janyewar.

Ya ce matakin ya biyo bayan kiran da suka samu ne daga fadar shugaban Najeriya a Abuja, inda aka neme su domin tattaunawa da ɓangaren gwamnatin jihar.

Ministan Ƙwadago na Najeriya, Cris Ngige, shi ne zai shiga tsakani a ganawar da za ta gudana da ƙrfe 10:00 na safiyar gobe Alhamis a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here