Advert
Home Sashen Hausa Ƙasashen Turai sun fi tallafa mana fiye da na Musulmai - Gwamna...

Ƙasashen Turai sun fi tallafa mana fiye da na Musulmai – Gwamna Zulum

Ƙasashen Turai sun fi tallafa mana fiye da na Musulmai – Gwamna Zulum

Gwamnan Jihar Borno Babagana Umara Zulum ya ce ƙasashen Turawa sun fi taimaka wa jiharsa fiye da Larabawa Musulmi yayin da suke fama da hare-haren ƙungiyoyin masu iƙirarin jihadi.

Zulum ya bayyana hakan ne a jiya Talata yayin da yake karɓar baƙuncin jakadan Falasɗinawa Saleh Fheied Saleh a Maiduguri, babban birnin jihar.

“Ni mutum mai aiki da zahiri, tun bayan da muka shiga cikin matsalolin nan, mun samu tallafi daga Birtaniya da sauran sassan Turai da Amurka da Canada da Japan da sauran waɗanda suka nuna damuwarsu garemu,” in ji gwamnan.

“Sai dai irin wannan tallafi bai taɓa zuwa daga ƙasashen Larabawa ba, waɗanda muke addini ɗaya (Musulunci) da kuma al’ada. Har Shuwa Arab muna da su a Borno, abin da ke nuna yadda tarihinmu ke da alaƙa.

“Mun yi yunƙuri iri-iri, mun je ofisoshin jakadancin ƙasashen Larabawa musamman masu arziki, amma da yawan ƙasashen Larabawa ba su damu da halin da muke ciki ba kuma ba su ba mu taimako ba.”

Gwamna Zulum ya kuma bayyana ziyarar jakadan da cewa mai “ƙarfafa gwiwa” kuma ya gode masa.

A nasa ɓangaren, Ambasada Saleh Fheied ya bayyana cewa akwai ‘yan asalin Jihar Borno a Falasɗin, ciki har da wata mai suna Fatima Barnawi da ta taɓa zama minista kuma babbar jami’ar ‘yar sanda.

“Akwai kamfanonin Falasɗinu da yawa a Najeriya da suke son yin aiki tare da gwamnatin Borno kuma za mu yi duk abin da kuke buƙatar mu yi domin taimakawa,” in ji jakadan.

Rikicin Boko Haram ya yi sanadiyyar kashe mutum fiye da 36,000 a jihohin arewa maso gabashin Najeriya tare da jawo asarar dukiya mai ɗumbin yawa cikin shekara fiye da 10.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

WA AKA RAINA, GWAMNAN KATSINA KO JAM’IYYAR APC?….Siyasar zaben 2023

WA AKA RAINA, GWAMNAN KATSINA KO JAM'IYYAR APC? . ..Siyasar Zaben 2023 Mu'azu Hassan @ Katsina City News Yanzu saura shekara daya da watanni a yi sabbin zabubbakan...

Bikin bada sandar girma a Masarautar Rano

Mai Girma Gwamna Dr. Abdullahi Umar Ganduje OFR, ya Jagoranci mika sandar Girma ga Mai Martaba Sarkin Rano, Amb. Alh. Kabiru Muhammad Inuwa Autan...

Majalisar Dinkin Duniya Ta Sake Nada Amina Muhammad Daga Jihar Gomben Najeriya Karo Na Biyu

Majalisar Dinkin Duniya, karkashin shugabancin Antonio Gutterres ta amince da sake nada Amina Muhammad, mataimakiyar sakatare janar na wasu shekaru biyar masu zuwa. An sake...

Cika shekara 22 da rasuwar Mamman Shata June 18, 2021

Cika shekara 22 da rasuwar Mamman Shata June 18, 2021 DAGA MUHAMMAD LAWAN RANO A YAU, 18 ga Yuni, 2021 Alhaji Dakta Mamman Shata Katsina, MON, ya...
%d bloggers like this: